Labaran Najeriya
Ka dakatar da N-Power, ka sanya kwararrun mallamai, Kungiyar NUT sun gayawa Buhari
Kungiyar Mallaman Makarantar Sakandiri sun bukaci gwamnatin Najeriya da dakatar da shirin sanya ma’aikatan N-Power don sanya kwararrun Mallamai a makarantu.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kadamar da wata shiri na samar da aiki ga ‘yan Najeriya, wadda ake kira N-Power da shugaban ya kafa ta jagorancin mataimakin sa Farfesa Yemi Osibanjo.
An kadamar da shirin ne don rage yawan rashin aiki a kasar ta wurin samar da ayuka ga ‘yan Najeriya 500,000 tun daga shekarar 2015 da gwamnatin ta shiga kan mulki.
Muna kuma da sani a Naija News da cewa shugaban wannan hidima ya gabatar makonnan da cewa gwamnatin na shirin don kara yawar mutane ga aikin N-Power, watau daga 500,000 zuwa yawar mutane Miliyan daya (1,000,000), don tabbatar da cewa sun magance rashin aiki a kasar da kuma tsarafa hanyoyin neman bida ga ‘yan Najeriya wajen tallafa wa matasa da ayuka da kuma kudi.
Shugaban Mallaman Makarantar Sakandari, Nasir Idris ya bayyana da cewa yawancin ma’aikatan N-Power da aka sanya a makarantu basu da wata kwararren fasaha wajen koyarwa.
Ya ce “Zai dace gwamnati ta dakatar da daukar ma’aikatan N-Power, amma ta kula da daukar kwararrun mallamai don koyawa ‘yan makaranta abin da ya dace” in ji Nasir.
“Makarantu sun kara raunana da rashin kwararun mallamai sanadiyar daukar mallamn da basu da fasahar koyaswa” inji shi.
“Akwai kwararun mallamai da ke bukatar a dauke su aiki, yin wannan zai fi kyau da daukar ma’aikata da basu da fasaha”.
Nasir Idris ya bayyana wannan ne a wata gabatarwa da yake da kungiyar a ganawa da suka yi cikin shekarar 2019.