Labaran Najeriya
APC: Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka Jihar Kano
Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyar APC ta Jihar Kano sun gabatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar don gabatar da hidimar yakin neman zabe a yau Alhamis 31, ga Watan Janairu, 2019.
Mun sami rahoto da cewa shugaba Buhari ya sauka a Jihar yanzunan, kuma jami’an tsaro ‘yan sanda da rundunar sojojin na zagaye a Jihar, musanman a shiyar da shugaban kasan zai yi gabatarwar ralin.
Mun sami tabbacin wannan rahoton ne daga shafin nishadarwa ta Bashir Ahmed, Sakataren yada labaran musanman ga shugaba Muhammadu Buhari.
bayanin na kamar haka:
President @MBuhari arrives the Ancient City of Kano, for his Presidential Campaign Rally this afternoon at the Sani Abacha Stadium. #PMBInKano pic.twitter.com/eGiRLrwk53
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) January 31, 2019
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Sabon Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya bada tabbaci ga ‘yan Najeriya da cewa jami’un su zata samar da kyakyawar shiri na tsaro ga zaben tarayya da ke gaba.
Ko da shike bayan ya fadi hakan, wasu ‘yan Najeriya sun mayar da martani akan zancen sa da barazanar da jami’an ke yi na kafa tsaro ga zaben 2019.
Fadin na kamar haka a turance: “We will do everything humanly, operationally and administratively possible to ensure buhari wins the election” is what you meant to say?
Wani kuma ya mayar da martanin nasa kamar haka
At the end of the 2019 elections, we are assuring the citizens that the Nigeria Police Force will be the Police of the year. We will do everything humanly, operationally and administratively possible to ensure a hitch free election. We will be neutral and apolitical pic.twitter.com/CDHTyP2YG5
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) January 30, 2019