Connect with us

Labaran Najeriya

Farfesa Wole Soyinka ya bayyana ra’ayin sa ga zaben shugaban kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanannen marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya gabatar da ra’ayin sa ga shugabancin Najeriya

Farfesan ya bayyana da cewa ba zai mara wa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba ko kuma shugaba Muhammadu Buhari da ke takaran kara komawa ga mulki.

Wole Soyinka ya gabatar da wannan ne awata tattaunawa da ake gudanar a yau da Farfesan ya halarta.

“Lokaci yayi da ruwa zata canza, lokaci yayi da ra’ayi zai canza, lokaci yayi kuma da zamu zabi wani dan takara dabam” in ji shi.

Duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari dan takaran Jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar dake takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP ne manyan ‘yan takara da ‘yan Najeriya suka san da ita, Farfesa Wole Soyinka ya nuna da cewa ba zai zabi ko daya ba daga cikin su.

Mun ruwaito a Naija News da cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce ko da shike Atiku Abubakar ba Almasihu bane, amma ya fi Muhammadu Buhari kirki har sau biyu.

Cikakken labari zai biyo baya…..