Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 5 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 5 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Yadda Atiku ya samu shiga Kasar Amurka

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu shiga kasar Amurka ne bayan an hada wata makirci na bad da sawu.

Muna da sani a Naija News da cewa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya samu shiga kasar Amurka ‘yan kwanaki da suka gabata bayan shekaru goma sha ukku (13) da aka hana shi da hakan.

2. Shugaba Buhari ya rantsar da shugaban hukumar ICPC, Bolaji Owasanoye da wasu mambobi

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Farfesa Bolaji Owasanoye a matsayin shugaban Hukumar Kwamitin Cin Hanci da Harkokin Halaka (ICPC).

Shugaba Buhari ya gabatar da wannan ne a ranar Litinin da ta gabata, ya kuma kaddamar da sabbin mambobi a Hukumar kuma ya rantsar da su duka.

3. Majalisar Dattijai ta janye karar Alkali Onnoghen (NJC)

Majalisar Dattijai sun bada umurni da cewa Kotun kara ta janye gwaji da kuma dakatarwa da aka wa babban Alkalin Kotun Najeriya, Walter Onnoghen.

Wannan ya auku ne bayan gwagwarmayan Hukumar Shari’a a kan batun.

4. Oshiomhole ya bayyana wadanda za su sayi NNPC daga Atiku inda ya hau mulki

Babban shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Adams Oshiomhole na zargin cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP na kokarin ne ya sayar da Kamfanin NNPC don tara jari da kuma samu suna ga ‘Yan Jarin Duniya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Atiku Abubakar ya rantse da cewa zai sayar da Kamfanin NNPC idan ya hau mulki, “Ko da hakan zai dauki rai na ne” inji shi.

5. Mayun kasar Najeriya sun goya wa Atiku baya ga shugabancin

Kungiyar Mayun Najeriya (AWWN – Association of White Witches in Nigeria) sun gabatar da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin zabin su ga shugabancin kasar Najeriya.

Kungiyar su bayyana hakan ne bayan ganawar su a tsaunin Obudu da kuma Zuma Rock a birnin Abuja.

6. PDP: Alkawalin Atiku Abubakar a Jihar Zamfara

Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya gabatar da cewa zai magance halin ta’addanci a kasar, musanman a Jihar Zamfara.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa, Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP sun gudanar da hidimar yakin neman zaben shugaban kasa a Jihar Zamfara, a ranar Litini 4 ga Watan Fabrairu, 2019.

Dan takaran yayi alkawali ga mutanen Zamfara da cewa zai samar da tsaro da kuma magance ta’addanci a Jihar inda an zabe shi a matsayin shugaban kasan Najeriya.

7. Ana shirin kaddamar da makirci don raunana zaben 2019 – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyaar Najeriya na zargin cewa ana shirye-shiryen makirci da tada zama tsaye ga sakamakon zaben 2019 da ke gabatowa, idan har shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019.

Lai Mohammed, Ministan Harkokin Watsa Labaru da Al’adu kasa ne ya gabatar da wannan zargin a taron manema labarai a da aka yi a ranar Litinin, Fabrairu 4, a nan birnin Abuja.

8. Oby Ezekwesili gabatar da murabus da tseren takaran Shugaban Kasa daga Jam’iyya ACPN

‘Yan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar ACPN, Oby Ezekwesili ta yi murabus da Jam’iyyar bayan janyewar ta a tseren takara a makonnai da ta wuce.

Mun samu tabbaci a Naija News da cewa Ezekwesili ta mayar ma Jam’iyyar ACPN katin mamba nata, da kuma duk wasu kayaykin da ta kumshi Jam’iyyar da ke a hannun ta.

9. Buhari na kan hanyar rasa kujerar mulki – Inji Kungiyar ‘Yan Shi’a

Kungiyar Darajja Addinin Musulunci (IMN) da aka fi sani da suna Shi’a sun bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari na kan hanayar rasa kujerar mulkin sa a kasar Najeriya.

Kungiyar sun bayyana wannan ne a babban birnin tarayya, Abuja, a ranar Litinin da ta gabata.

Ka samu cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa