Labaran Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya hada Liyafa tare da ‘yan Jam’iyyar APC a daren Jiya
A daren jiya, Litinin 5 ga Watan Fabrairun, Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya wata zaman cin Liyafa ga mambobin Jam’iyyar APC a birnin Abuja.
Ko da shike muna da sani a Naija News da cewa Shugaba Buhari ya yi ganawar Kofa kulle tare da ‘yan Jam’iyyar bayan liyafan.
Zaman Liyafan ta halarci Babban shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Adams Oshiohmole, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Mataimakin kakakin yada yawun Jam’iyyar, Yusuf Lasun da Babban shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila hade da wasu ‘yan Jam’iyyar APC da ba a bayyana sunayen su ba.
Mun sami tabbacin wannan liyafan ne kamar yadda aka aika a shafin nishadarwa ta twitter
PHOTOS:
Last night, President @MBuhari had dinner with APC House of Rep members and candidate for 2019 election. pic.twitter.com/KcRWk5DIen
— Government of Nigeria (@AsoRock) February 5, 2019
An gabatar da cewa Shugaban ya yi zaman tattaunawa akan zaben 2019 da jam’iyyar bayan sun gama cin liyafar.