Labaran Najeriya
Buhari ya kasa, Kuma dole ne a tsige Atiku idan shi ma ya kasa – inji Dele Momodu
Wani babban Mai Kudi, shugaban Gidan Yada Labaran ‘Ovation Internation’ da kuma dan sana’a, Mista Dele Momodu ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rigaya ya kasa a shugabanci, a nashi gani.
“Muhammadu Buhari ya kasa ga shugabancin kasar nan a gani na, kuma babu wanda zai canza wannan gani da kuma ra’ayin nawa” inji shi.
“Ko da shike Buhari ya kasa, Duk da haka idan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, shi ma ya kasa ko aiwatar da halin da bama so, dole ne a tsige shi” inji Dele Momodu.
Muna da tabbacin wannan bayyanin ne a Naija News Hausa kamar yadda Dele Momodu da kanshi ya aika a yanar gizon nishadarwa na twitter, a yayin da yake mayar da martani ga wata zargi da wani ke masa a shafin twitter.
Ga bayyanin kamar haka;
Ko da shike wani ya mayar da martani akan wannan bayani na Dele Momodu. Karanta a kasa; A turance.
Everyone is my friend, including you, I have very very close friends and big brothers in APC but Nigeria is far more important to me than personal relationships; in my view BUHARI has failed and no one can change that and if ATIKU fumbles, he must be sacked with ignominy… https://t.co/GRQgJOyXyJ
— Dele Momodu Ovation (@DeleMomodu) February 6, 2019
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa, Jennifer Atiku Abubakar, matan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ta bukaci Mata da Matasa su jefa wa mijin ta kuri’un su ga zaben 2019 don magance matsalar Jintsi da samar da ayuka a kasar Najeriya.