Uncategorized
Wata Macce da ta tsage cikin ta da Reza a Jihar Bauchi ta Mutu
Wata mumunar abu da ya auku a Jihar Bauchi a yayin da wata matar gida da tare da ciki ta tsage cikin na ta da reza wai don zafin na’uda.
Mun samu rahoto a Naija News Hausa na da cewa abin ya faru ne a ranar 27 ga watan Janairu, 2019. Macce mai suna Hassana Muhammadu da ke da shekaru 42 a Kauyan Bedi, a karamar hukumar Ganjuwa, a Jihar Bauchi ta tsage cikin ta da reza don zafin na’uda kamar yadda muka samu tabbacin haka.
An bayyana da cewa matar na da yara bakwai ne kamin wannan cikin da ta mutu da shi a gidan mijin ta mai suna, Mallam Maikudi Muhammadu.
“Har yanzu ban yi tsanmanin mata na zata iya aiwatar da irin wannan mugun hali na dauke rayuwarta da kanta ba” inji Maikudi, Mijin Hassana.
“Na samu kira ne daga wani makwabcin mu da cewa matata na bukatar in dawo gida saboda bata jin dadin jikinta ko kadan. Isa na a gidan sai na cin mata cikin zafin na’uda, ganin hakan sai na haura da kiran mai kulawa da karban haifuwa a yankin, amma mata na bata yadda da hakan ba, ta ce in kira mata kanuwar ta dan ta zo ta kula da ita” inji shi.
“Ko da isar mu a gidana tare da kanuwar, tana shiga dakin sai na ji ihu, in shiga dakin sai ga mata na cikin bulbulan jini sakamakon tsage cikin ta da ta yi da reza don zafin na’uda”
“Ganin hakan sai na kira mai anguwa ya taimaka mani da motar da zamu kai ta a asibiti don kulawar gaggawa. Daga nan muka kaita a asibitin Abubakar Tafawa Balewa da ke a nan garin Bauchi saboda irin bukatar kulawa ta gaggawa da ta ke so” inji Maikudi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wani mutum mai suna Oare Abdulrazak, ya yi wa matarsa duka wai don bata gayar da kishiyarta ba.
“Abin bakin ciki gareni, muna isa asibitin sai ta mutu. daga nan kuma muka dauki matakin bizine ta a hanyar musulunci”
An bayyana ga manema labarai da cewa, Hassana ba ta hurda da matan da ke a kauyan balle ma wani ya san matsalar da ta ke ciki” inji bayanin wani mazaunin kauyan.
Mallam Muhammad Idris, Mai anguwar kauyan ya nuna bakin cikin shi da wannan mugun abin, ya kara da cewa “Irin wannan mumunar abu bai taba faruwa a kauyan Bedi ba” in ji Shi.