Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 6 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 6 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Shugaba Buhari ya nemi haƙuri da fahimtar jama’a akan zancen sabon albashin ma’aikata

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ma’aikatan Najeriya da yin hakuri da fahimta yayin da yake kula da al’amurran sabon tsarin albashin ma’aikatar kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a wata zama da suka yi tare da ‘yan kasuwa na kasa da kasa (NLC) a ranar Talata a birnin Abuja.

2. Hukumar ASUU ta gudanar da zaman tattaunawa akan yajin aiki da a ke ciki

Hukumar Mallaman Jami’o’i (ASUU) a ranar Talata ta da ta gabata, sun gudanar da wata zaman tattaunawa na kulawa da zancen ko su dakatar da yajin aikin da kungiyar ta fara watannai ukku da nan, ko kuma su ci gaba da yajin aikin.

Wannan zaman tattaunawar, sakamakon kira ne daga shugaban Hukumar na bukatar su gana don daukar mataki akan yajin aikin. kamar yadda muke da tabbacin haka a Naija News.

3. Tambuwal ya tsige wani Kwamishana wai don ya koma ga Jam’iyyar APC

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal a ranar Talata, Fabrairu 4, ya dakatar da Kwamishinan Bayanai, Mr Bello Muhammad-Goronyo, wai don ya koma wa Jam’iyyar APC.

An gabatar da hakan ne daga bakin Daraktan Watsa Labaru da Harkokin Jama’a, Malam Abubakar Shekara, ranar Talata da ta wuce.

4. Babu wata garin da Boko Haram ke kame da shi – inji Rundunar Sojojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya, Rukunin Operation Lafiya Dole ta ta yi watsi da jita-jitar da ake yi a kan yanar gizo cewa na cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun kame garuruwa biyar.

Jita-jitan da ya bi ko ta ina a yanar gizo a ranar Talata da cewa Boko Haram sun kame garuruwa biyar ba gaskiya bane.

5. Shugaba Buhari a Jihar Ekiti ya yi kurewar fadin cewa ya hau mulki a shekarar 2005

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Talata da ta gabata, ya sake wata raguwa kalma a yayin da Jam’iyyar APC ke hidimar ralin shugaban kasa a Jihar Ekiti. shugaban ya ce shi da jam’iyyarsa, APC sun fara mulki a shekara ta 2005, maimakon ranar 29 ga Mayu, 2015 da suka shiga mulki.

Ko da shike muna da sani a Naija News Hausa ne da cewa shugaba Muhammadu Buhari na son ne ya tunawa jama’a da cewa Jam’iyyar sa bata manta da alkawalan da ta yi ba a shekarar 2015 da suka hau mulki a kasar.

6. Gwamna Ambode ya gabatar da kasafin kudi Jihar Legas, Naira biliyan N852bn ga ‘yan Majalisa

A ranar Talata da ta gabata, Akinwunmi Ambode, Gwamnan Jihar Legas ya gabatar da kasafin kudi ta 2019 na N852.316b a gaban ‘yan majalisar dokoki a gidan majalisar dokokin jihar.

Naija News Hausa na da tabbacin hakan.

7. ‘Yan Shi’a sun ce suna a shirye su mutu domin El Zakzaky

‘Yan kungiyar musulunmai (IMN), da aka fi sani da suna ‘yan Shi’a, a yau sun gabatar da shirin su na bukatar sakin jagoransu, Sheik Ibrahim El-Zakzaky.

‘Yan Shi’ah sun yi rantsuwa da cewa ba za su ja dabaya ba har sai shugabansu da matarsa, Zeenat sun kubuta daga tsarin da gwamnati tarayya ta yi masu tun shekarar 2015.

8. ‘Yan Hari da Bindiga sun kashe Yayar Kabiru Marafa, Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta tsaka

Wasu mahara kimanin mutum dari sun fada wa kauyan Ruwan Bore da hari har sun kashe ‘yar uwar Kabir Marafa, Sanatan da ke wakilcin yankin Zamfara ta Tsaka, sun kuma sace Mijinta.

A bayanin wani mai suna Abubakar Tsafe ga manema labarai, Ya ce “Maharan sun fada wa gidan Sanatan ne inda ‘yar uwansa ke zama a Ruwan Bore ta karamar hukumar Gusau a yau Talata” Abubakar ma’aikaci ne a gidan Sanata Marafa.

Ka samu cikkaken labaran Najeriya daga shafin Naija News Hausa