Connect with us

Labaran Najeriya

Bayyanin shugaba Buhari wajen rattaba hannu ga takardar Zamantakewa ta Lafiya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Laraba, 13 ga Watan Fabrairu, An kara rattaba hannu ga takardar yarjejeniyar zaman lafiyar kasa ga zaben 2019 a birnin Abuja.

Hidimar ta halarci manyan shugabannan kasar Najeriya kamar su; Abdulsalami Abubakar, Mahmood Yakubu, Bishof Mathew Kukah, Yakubu Gowon da manyan baki daga kasar Afrika da Turai.

1. Yayi bayani game da Uzuri

Shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa ya kula da irin uzuri da mutane ke ciki ga zaben wannan shekara ta 2019. Ya ce a zabe irin wannan, ba abun mamaki bane ne da ganin cewa mutane na cikin uzurin da zafin zuciya, “amma bukatar kasar Najeriya itace a gama zabe lafiya” inji shugaba Buhari.

2. Ya kafa baki ga yaduwar Mata da Matasa ga Zaben 2019

Shugaba Buhari ya bayyana da cewa dokar da ya sanya hannu kwanakin baya a shekara ta 2018, na cewar Matashi ko Matashiya na da daman takara a kasar ya taimaka wajen karuwar jama’a ga zaben 2019.

Haka kuwa Jam’iyyun siyasa sun karu kwarai da gaske bisa ga yadda take a da.

3. Ya shawarci mutane da kara kokari wajen ayukan siyasa

Buhari ya kula da cewa harwa yau akwai mutanen da basu damu da harkan siyasa ba. Ya bada shawara da cewa ya kamata Maza, Mata da Matasa su kara kokari da gwagwarmaya wajen aikin zabe don cin gaban kasa da kuma shugabanci ta kwarai.

4. Batun Rattaba hanu ga Takardar zaman lafiyar kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa Rattaba hannu ga takardan yarjejeniyar zaman lafiyar kasa da aka yi a yau abu ne mai muhimanci da gaske. “Anyi wannan ne kuma don tabbatar da cewa kowa ya bada hadin kai da kuma tabbatar da cewa babu tashin hankali ga zaben 2019” inji shi.

Ya kara da cewa Hukumar INEC kuma na kokarin magance kowace irin halin makirci ga zaben 2019.

5. Shawara ga Matasa

Shugaba Buhari ya shawarci Matasa da cewa su guje daga kowace irin halin tashin hankali da ta’addanci ga zaben 2019.

“Kada ku yadda wani dan siyasa ya yi amfani da ku don kadamar da halin ta’adanci ga wannan zabe” inji Buhari.

6. Gaisuwar Ta’aziyya ga Mutanen da suka rasa ‘yan uwar su

Shugaba Muhammadu Buhari ya karasa da bayyana bakin cikin sa ga wadanda suka rasa rayukan su a wajen yakin neman sake zabe a Jihohin kasar. Yayi addu’a da cewa Allah ya jikan su.

Ya karasa da shawartan matasa da cewa shu fita don jefa kuri’a a ranar Asabar da kuma zaban dan takara da suke so.

Karanta wannan kuma: Leah Sharibu ba ta Mutu ba – inji Gwamnatin Tarayya

Kali bidiyon yadda shugaban Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya jefar da Tutar Jam’iyyar