Connect with us

Uncategorized

Ku guje wa Makirci wajen aikin Zabe, Kazaure ya fada wa ‘Yan Bautan Kasa (NYSC)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Kwana daya da awowi kadan ga zaben tarayya ta kasar Najeriya, Darakta Janar na ‘Yan Bautan Kasa (NYSC0, Maj. Gen. Suleiman Kazaure, ya jawa ‘yan bautan kasa kunne da cewa su guje wa duk wata halin banza wajen gudanar da aikin zaben 2019, musanman karban cin hanci da rashawa.

“Idan kun karya dokar aikin zaben kasa, za ku je gidan jaru” Kazaure.

Muna da sani a Naija News da cewa Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC sun bada dama ga wadanda ke bautan kasa, watau NYSC don taimakawa wajen gudanar da ayukan zaben 2019 ta Najeriya.

Kazaure yayi wannan gabatarwar ne ta bakin kakakin yada yawun sa ga lamarin zabe, Sadiq Ipaku, Insfekta na Hukumar NYSC ta birnin Abuja.

“Kasa ta kira ku a cikin bauta, don ku taimaka wajen gudanar da ayukan zabe, zai ci kyau ace kun gudanar da shi yadda ya dace” inji shi.

“Ku kasance a tsare, da kula da kuma kwanciyar hankali wajen gudanar da ayukan ku” inji Mallam Abubakar Mohammed, Kadineta na hukumar NYSC ta Jihar Adamawa .

“Za a samar da isashen tsaro a gareku: inji Mohammed.

Karanta wannan: Jami’an Yan Sanda sun kame Masu Sace-Sacen Yara a Birnin Abuja