Labaran Najeriya
APC: Ibrahim Modibbo ya janye daga Jam’iyyar GDPN, ya komawa APC
Alhaji Ibrahim Modibbo, mataimakin dan takaran shugaban kasa ga tseren zaben 2019 na Jam’iyyar GDPN, yayi murabus da Jam’iyyar ya komawa Jam’iyyar APC don marawa Jam’iyyar da shugaba Muhammadu Buhari baya ga zaben ranar Asabar.
“Da irin gwagwarmaya da kokarin da shugaba Muhammadu Buhari yayi tsakanin shekaru ukku da watannai a mulki, ya dace a saken zaben shugaban da kara mulkin kasar Najeriya” inji Modibo.
Mun samu tabbaci ne a Naija News da cewa Modibbo ya janye ne daga Jam’iyyar GDPN a ranar Talata, 12 ga Watan Fabrairun da ta gabata a birnin Abuja don marawa shugaba Buhari baya ga tseren takaran.
“Na sadaukar da matsayina ne na mataimakin dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar GDPN don marawa shugaba Buhari baya ga zaben 2019, ganin irin kokari da ayukan da shugaban yayi a gwamnatin sa tun daga shekarar 2015 da ya hau mulki” inji Modibbo.
Ya ce; “Shugabancin Buhari cikin shekaru ukku da watannai ya nuna da cewa zai i kyau idan an sake zaban sa ga mulkin kasar Najeriya. Musanman ayuka da ya samar da kuma karfafa tattalin arzikin kasar” inji shi.
“Na kuddura da mara wa shugaban baya saboda na gane akwai bukatar hakan” inji bayanin Modibbo.
Karanta wannan kuma: Duk wanda ya ce Buhari da Osinbajo basu yi kokari ba, lallai bai ga wannan duniyar, inji Olubisi Osinbajo, Mamman Farfesa Yemi Osinbajo.