Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun sace mutane 11 a Jihar Rivers

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan hari da bindiga a Jihar Rivers sun hari wata motar Toyota Sienna SUV da ke kan tafiya daga hanyar Abuja zuwa Port-Harcourt, inda suka tare motar, suka kuma sace direban tare da fasinjoji goma (10) dake cikin motar, anan karamar hukumar Abua – Odual.

Muna da sani a Naija News da cewa hare-hare ya soma yawa a Jihar Rivers. A baya mun ruwaito da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace ciyaman na Jam’iyyar APC a wata yankin Jihar Rivers.

Mun samu rahoto ne da cewa ‘yan hari da ke sanye da abin rufe ido sun fada wa motar ne da hari a anan mahadin hanayar Rumuekpe da ke nan Emohua, karamar hukumar Jihar.

“Maharan sun fito ne daga cikin daji suka fada wa motar da hari, suka kuma sace direban motar da fasinjoji da ke ciki” inji wani mazaunin shiyar da ke da sanin yadda abin ya faru.

Ko da shike bai bayyana sunan sa ba, amma ya bayyana da cewa sun fito ne daga cikin dajin da harbe-harben bindiga, daga nan suka sace mutanen da ke cikin motar hade da direban sa.anan suka bar motar suka wuce” inji shi.

“Na cinma motar Sienna din ne da safiya misalin karfe 9 na safe, sa’an da na dawo kuma misalin karfe 11, na kara cinma motar a wajen” inji shi.

“Na san direban, mukan kira shi da suna ‘Star’. Mun yi kira ga taimako da muka gane da abin da ya faru, ina kuma addu’a ga Allah ya sa da shi da fasinjojin sun kubuta daga wannan harin” inji shi.

A yayin da aka karbi rahoton nan, kakakin jami’an tsaron Jihar, Mista Nnamdi Omoni, ya fada da cewa bai samu cikakken bayyani ba tukunna game da harin.

 

Karanta wannan kuma: Dan takaran Sanata a Jihar Kwara ya kure mutuwa sakamakon harbin ‘yan hari da bindiga