Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan sun kame Sanata Rafiu Ibrahim a Jihar Kwara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an ‘yan sandan Jihar Kwara sun kame Sanata Rafiu Ibrahim akan zargin kadamar da farmaki a Jihar.

‘Yan awowi kadan da fara zaben shugaban kasa da ta gidan majalisa, jami’an tsaron ‘yan sandar Jihar Kwara sun kame Rafiu Ibrahim, Sanatan da ke wakiltar Jihar Kwara ta Kudu akan zargin cewa Rafiu ne ya jagoranci wata farmaki da ta dauke rayuka 2 a ranar Talata da ta gabata a Jihar.

“Mun kira shi don bincike, kuma yana nan hake a Ofishin mu tun ranar Alhamis don bayar da cikakken bayani akan zargin” inji kakakin yada yawun jami’an ‘yan sandan Jihar, Mista Ajayi Okasanmi a bayanin sa ga manema labaran PREMIUM TIMES a safiyar ranar Jumma’a.

Da aka bukaci kwamishanan ‘yan sandan Jihar, Mista Kayode Egbetokun da bayanin akan lamarin, ya fada da cewa ba zai iya bada wata bayani ba a wannan lokacin game da kame Sanata Rafiu.

Mun samu rahoto ne da cewa ana zargin Mista Rafiu Ibrahim ne akan cewa shi ne ya jagoranci farmaki da ‘yan ta’adda suka kai wa Mista Lola Ashiru, watau dan adawan sa daga Jam’iyyar APC a Jihar Kwara ta Kudu.

Mun gane a Naija News Hausa da cewa Rafiu dan Jam’iyyar PDP ne shi.
Magoya bayan sanatan, sun zargi jami’an ‘yan sanda da kame shugaban su Mista Rafiu Ibrahim da barin dan takaran kujerar sanata daga Jam’iyyar APC, Mista Ashiru da ci gaba da gudanar da nasa hidimar neman zabe don neman kuri’u ga zaben gidan majalisa da za a yi hade da ta shugaban kasa ranar Asabar ta gaba.

“Wannan matakin ya sa dan takaran mu bai samu damar yawon neman zaben sa ba” inji ‘yan Jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Sanata Rafiu a tseren kujerar Sanatan yankin Jihar” inji su.

Karanta wannan kuma: Dan takaran Sanata a Jihar Kwara ya kure mutuwa sakamakon harbin ‘yan hari da bindiga