Connect with us

Uncategorized

A dakatar da sanar da sakamakon zabe – inji Shehu Sani

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yayin da hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ke gabatar da zaben shugaban kasa na jihohi, dan takaran na Jam’iyyar PRP, Shehu Sani ya bukaci hukumar INEC da dakatar da gabatar da sakamakon zabe.

Shehu ya gabatar da hakan ne ga manema labarai da zargin cewa rahotanni da ake gabatarwa ba daidai bane a wasu wurare, da kuma zargin wata rikici akan zabe.

A halin yanzu babu cikakken bayani akan ko wace irin rikici ne yake nufi, ko kuma ina ne aka kirga zabe fiye da yawar kuri’u, amma Sanata Shehu ya dage da cewa akwai matsala wajen kirgan zabuna.