‘Yancin El-Zakzaky Baya A Hannun El-Rufai Yake ba – IMN Sun fada wa Gwamnatin Buhari

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wacce kuma aka fi sani da suna Shi’a, ta yi Allah wadai da bayanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa ‘yancin shugabanta, Ibrahim El-Zakzaky ya dangana ne a hannun gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

Naija News ta tuno cewa yan Shi’a sun yi kiran a saki El-Zakzaky ne bayan sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

Amma a wata sanarwa da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari ta bayar, suna mai cewa sakin jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) Ibrahim El-Zakzaky, ya dogara ne kawai ga gwamnatin jihar Kaduna.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da Shi’a a ranar Laraba da ta gabata sun halarci hidimar coci ta Kirsimeti a wasu sassan arewacin Najeriya.

A cocin daban daban na Advent, Samaru, Zariya, jim kadan bayan kammala hidimar, shugaban kungiyar, Farfesa Isa Hassan-Mshelgaru ya ce muhinmancin halartar wannan hidimar shine inganta soyayya, hakuri da fahimta a tsakanin yan Najeriya.

‘Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Sace Yara Uku Na Mista Obi a Jihar Kaduna

Mugun yanayi ya sanya wani dan kasuwa a Kaduna, Christian Obi kuka da hawaye a ranar Alhamis bayan da wasu ‘yan bindiga sun sace yaransa uku.

Mutumin yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Sabon Tasha, Kaduna, ya ce ya ga wadanda suka sace yaran ne sanye da kayan sojoji a cikin gidansa amma sai ya shiga buya.

Dan kasuwan ya lura cewa ya ga yadda barayin suka kwashe yaransa uku zuwa wani wurin da bai san da shi ba amma ya kasa magana don tsoron kada a kashe shi ko kuma a tafi da shi.

“Nan da nan da na hange su ta cikin gilashin gida na, na san cewa su sojoji ne na karya. Na je in ɓoye wani wuri a cikin gidana amma na ci gaba da bin matakansu. Na ga suna kwashe ‘ya’yana uku. Na kasa iya daga murya, amma a cikina, na kasance cikin hawaye da bacin zuciya” inji Mista Obi.

Mutumin wanda ya yi rayuwansa a Kaduna da tsawon shekaru 38 ya ce yaran da aka sace sun hada da Jonathan  dan shekara (31), Joachim (28) da kuma Benjamin mai shekaru (21).

Ya kuma kara da cewa har yanzu ‘Yan Bindigar ba su yi kira ba tukuna don gabatar da bukatarsu.

Wani shaidan gani da ido wanda ta bukaci kada a bayyana sunan nata ta ce ta samun ganin yadda abin ya gudana a yayin da ita ma ke a boye.

“Na ga maza uku, biyu na sanye da kayan sojoji kuma na ji suna magana da harshen Hausa.”

“Sun fada gidan ne ta yin tsalle kan shingen gidan. Daya daga cikin abokaina ne ya lura lokacin da wani a cikin su ya yi tsalle a cikin gidan, A yayin da wani shima ya bi baya.

“Suna ta zagayen gidan da neman hanyar shiga gidan amma sun kasa.”

“Daga dakin wanki ne suka samu yin tsalle da shiga cikin gidan ta wani karamin wuri a kofar, dukkan mu kuwa muka gudu da shiga dakin ‘yan mata don boyewa.”

“Lokacin da suka shigo, Jonathan ya gaya masu duk abin da suke so zai ba su. Ya ba su kudi kuma sun karɓa, duk hadi da wayoyinsu amma na samu ɓoye nawa,” in ji ta.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya ce ya na sane da yanayin).

“Ee muna sane da satar Ni. Ina kan aiki tukuru kan lamarin, kuma za a sanar da hakan ba ba da jimawa ba.

Ba Mu Gama Da Siyasa Ba Tukunna, Muna Nan Dawo Wa A Shekarar 2023 – Shehu Sani

Tsohon Sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani a ranar Laraba ya yi alfahari da cewa bai janye daga siyasa, yana nan dawo nan da shekarar 2023.

Shehu ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Kaduna lokacin da kungiyar Magabata na Sabon Garin Nassarawa suka ba shi wata kyautar lambar yabo don kyakyawan aikinsa da kuma halin karimci ga wakilcin al’umma.

Naija News Hausa ta tuno da cewa Sanata Shehu Sani ya rasa kujera ta Sanata ne ga Sanata Uba Sani, wani na hannun dama ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai, a zaben 2019.

A lokacin ne gwamna El Rufai ya yi alfahari da cewa shan kayen Shehu Sani na nufin cewa ya yi ritaya daga siyasa, bashi ba siyasa kuma.

Amma da wannan zance na Shehu Sani, mai cewa “Ba mu gama da siyasa ba tukunna, za mu ko dawo”. wannan zancen tayi hannun riga da alfaharin gwamna El-rufai.

A cewar Shehu, “bamu da fargaba ga komai, kuma babu abinda da zai tsoratar damu daga shiga takara a 2023. Lokacin da mutanenmu suka nemi mu dawo, zamu koma”.

A yayin nuna godiya da kyautar karramawar, Shehu Sani ya ce ya yi alfahari da shugabancin aiki a Majalisar Wakilai ta kasa, kuma kyautar da aka ba shi “shaida ce ta ingancin wakilcinsa” a zaman dan majalisar dattijai a babban majalisa na 8.

“Majalisa na 8 sun sami damar kare mutuncin majalisar dokoki da ‘yancinsu kuma sun dage kan kare dimokiradiyya; bincike kan amfani da iko, zartarwa da aiwatar da su kan tsarin mulki da aikinsu ba tare da tsoro ko neman alfarma ba” inji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Sanata mai wakiltcin Gombe ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Muhammad Danjuma Goje, ya sanar da aniyarsa na janyewa daga kara tsayawa takara a nan gaba.

Tsohon gwamnan jihar Gombe din ya bayyana hakan ne a yayin wata hidima mai taken ‘Goje Empowerment Programme’ wadda ya gudana a filin wasa na Pantami a Gombe.

Duk da haka, Goje ya ce zai ci gaba da taka rawar gani a fagen siyasar jiha da na kasa baki daya.

Muna Zantawa Da Buhari Kan Yanayin El-Zakzaky – Gwamnatin Iran

Iran Ta Tattaunawa Da shugaba Buhari Kan Zancen El-Zakzaky

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa tana cikin tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, IMN, da aka fi sani da ‘Yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Abbas Mousavi, ya ce kasar tasu ta hanyar diflomasiya, tana hulda da gwamnatin Najeriya kan yanayin halin da El-Zakzaky ke a ciki.

Mousavi a hirar ya fadawa manema labarai a Tehran, babban birnin Iran a ranar Lahadin da ta gabata cewa Shugaba Buhari da Mataimakin Shugaban Harkokin tattalin arzikin Iran, Mohammad Nahavandian, sun gana kwanan nan a Malabo, Equatorial Guinea, kuma sun tattauna kan batutuwa da dama, ciki har da batun El-Zakzaky.

Taron ya gudana ne a yayin taron kolin kungiyar kasashen waje na fitar da Gas (GECF) a Equatorial Guinea.

Jami’in ya kara da cewa “Muna fatan cewa shawarwari da shirye-shiryen da ake yi tare da gwamnatin Najeriya za su yi cinma buri a gagauci wajen warware wannan matsalar ta El-Zakzaky,” in ji jami’in na Iran.

Naija News ta tuna cewa El-Zakzaky yana a tsare tun Disambar 2015, bayan shi da magoya bayan sa suka yi artabu da sojojin Najeriya a cikin jerin gwanon Hafsan Rundunar Sojojin kasar, Tukur Buratai, a cikin Zariya a jihar Kaduna.

Bayan haka, hukumar DSS a ranar Jumma’a da ta gabata ta dauki El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat daga Ma’aikatarta zuwa Gidan Horon Al’umma da ke a Kaduna, kamar yadda Babban Kotun Jihar Kaduna ta umarce su da yi.

‘Yan Bindiga sun Kashe Mutane Hudu a Yayin Kallon Gasar Wasan Kwallon Kafa a Kaduna

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar, wacce Naija News Hausa ta samu a sanarwa, ta ce wasu mutane dauke da makamai sun harbe mutane hudu tare da raunata wasu hudu a wani hari a filin wasan kwallon kafa a kauyen Zunuruk na karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.

Rahoton ya bayyana da cewa Maharan sun kai hari ne a ranar Lahadin da ta wuce da yamma yayin da matasa suke kallon wata gasar kwallon kafa.

Wani shaida, wanda ya bukaci kada a sanar da sunansa ya ce maharan sun fito ne daga cikin wani daji da ke kusa da wajen, inda suka yi harbe harben bindigasu har da ya kai ga kashin mutane hudu a take.

Mai shaidar ya ce ci wannan lamarin ne ya kawo karshen wasan kwallon kafar yayin da masu kallo duka suka gudu don tsira da rayukansu.

Ya kara a cikin bayaninsa da cewa a wani kauyen Tsonje da ke kusa da shiyar, a safiyar ranar Lahadi din a yayin da mutanen garin suka farka da safiya sun gano gawar wani daga cikin mazaunin yankin da ya mutu sakamakon harbe-harben.

Ya ce wanda aka kashe din, mai suna Dogara Kazzah ya fita ne da dare a misalin karfe takwas na dare don yin fitsari a bakin daji a daren, amma bain takaici ba a ga dawowarsa ba, kawai ne an iske gawar jikinsa da safiyar sakamakon harbin bindiga a kashegarin Lahadi.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci Asibitin Kafanchan da misalin karfe 10:30 na dare, an ga motar asibiti tana dauke da mutane uku daga cikin wadanda suka jikkata zuwa Kaduna bayan samun taimako na farko.

Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna Sun kama Mutane 8 da Zargin Kisa Da Kona Wani Mutum

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kama mutum takwas da ake zargi da hada hannu a kisan wani mai suna Mujtaba Saminu, wanda aka kashe da kona shi har ga toka a kauyen Chibiya da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

A cewar ‘yan sanda, an riga an mika karar zuwa Sashin Binciken Laifuka (CID) don gudanar da bincike kan yanayin da ya haifar da aikata laifin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Yakubu Sabo, wanda ya tabbatar da kamo wadanda ake zargin ya ce za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.

Naija News Hausa ta kula da cewa marigayi Mujtaba Saminu, dan asalin garin Kachia, bawai an sace shi bane kamar yadda ake yadawa a labarai tun ranar Lahadi 10 ga Nuwamba, 2019, da cewa ya bace a garin Chibiya na karamar hukumar Kajuru, ashe ba a sace shi aka yi ba kamar yadda ake tsammani, kashe shi aka yi da kuma ƙona shi har ga toka, aka kuma zubar da gawarsa a cikin wani dan kabari.

Wata majiya ta bayar da cewa marigayin ya tafi ƙauyen ne don siyan Gurjiya, tun daga wannan lokacin ba a kara ganinsa ba har sai da aka gano gawarsa ƙone a cikin wani kabari mara kyau a ƙauyen.

Jami’in Hulda da Al’umma ta ‘yan sandan (PPRO) ya yi bayanin cewa, “Ee da zarar mun sami labarin kisan, sai Jami’in‘ Yan Sanda a Kajuru suka tuntubi wasu shugabannin gargajiya a yankin kuma nan take aka sami damar kama mutane 8 da ake zargi da hadin hannu a kisan mutumin.”

KARANTA WANNAN KUMA; Rikici Ta Barke Tsakanin Yarbawa Da Hausawa a Jihar Osun.

Shugaba Buhari Ya Bar Daura Zuwa Jihar Kaduna A Yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya bar garin sa Daura, cikin jihar Katsina bayan kammala ziyarar kadamarwa ta aiki ta kwanaki biyar.

Naija News ta rahoto cewa Buhari ya bar Daura ne da safiyar ranar Talata kuma ya sauka a Filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua akan helikofta.

Shugaban ya samu karban marabta daga Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari; Mataimakinsa, Mannir Yakubu, da Shugaban Majalisar Dokoki ta Jiha, Tasi yake Maigari.

Sauran wadanda suka marabci shugaban sun hada da Sakataren Gwamnatin Jiha, Dakta Mustapha Inuwa; Shugaban Jam’iyyar APC ta reshen jihar Katsina, Shitu Shitu; da Alkalin Kotun jiha, Mai shari’a Musa Danladi, da Shugabannin Ma’aikata na Jiha da membobin Majalisar zartarwa ta Jiha.

Daga nan, jirgin saman shugaban kasan ya tashi daga tashar jirgin sama da misalin karfe 10:23 na safe zuwa jihar Kaduna inda ake sa ran zai halarci taron Babban Hafsan Sojojin shekara da shekara.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Buhari Ya Kadamar Da Bude Sabon Makarantar Jami’ar Sufuri A Jihar Katsina

A ranar Litinin din da ta gabata ne Shugaba Buhari ya yi bikin bude makarantar jami’ar sufuri a Daura, inda kuma ya jagoranci bude hanyar Kwanar Gwante, wacce ke kan hanyar Kano zuwa Daura.

Kalli Hotuna a kasa;

Kotu Ta Dakatar da ‘Yan Majalisar PDP Biyu a Kaduna, Ta Bada Umarnin Sake Zabe

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a jihar Kaduna ta sallami wasu mambobi biyu a majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata.

‘Yan Majalisa biyun suna wakilci yankin Kagarko da Sanga bi ne a majalissar dokokin jihar Kaduna.

Naija News ta fahimci sunan ‘yan majalisa biyun da a kora da, Mista Morondia Tanko mai wakiltar mazabar Kagarko da Malama Confort Amwe na mazabar Sanga duka biyu a dandalin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A bayan da Kotun ta koresu ta kuma umarci Hukumar Zabe na Kasa (INEC) da ta gudanar da wani sabon zabe domin tantance wanda zai wakilci mazabar Kagarko da Sanga a cikin majalisun jihar, in ji rahoton NAN.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Bishop na Zariya Diocese (Anglican Communion), Rt Rev Abiodun Ogunyemi ya yi ikirarin cewa gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna ba zai taba ci nasara ga fito takarar shugabancin Najeriya ba.

Bishop din ya bayyana cewa ya fadi hakan ne da yin imanin cewa gwamnan jihar Kaduna ya shirya domin takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.

Bazaka taba zama Shugaban Kasar Najeriya ba – Bishop ya fadawa El-Rufai

Bishop na Zariya Diocese (Anglican Communion), Rt Rev Abiodun Ogunyemi ya yi ikirarin cewa gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna ba zai taba ci nasara ga fito takarar shugabancin Najeriya ba.

Bishop din ya bayyana cewa ya fadi hakan ne da yi imanin cewa gwamnan jihar Kaduna ya shirya domin takara a 2023.

Naija News ta fahimta da cewa Ogunyemi ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake mayar da martani ga shirin da gwamnan yayi a kwanakin da suka gabata na rushe gidan St George Cathedral mai tsawon shekaru 110 da aka gina, wanda ke a Sabon-Gari Zariya da kuma wani shirin da ake zargi na rushe kadarorin Cocin da ke a Sabon gari.

Bishop din a shafin intanet na Iklisiyar ya la’anta Bishop din Wusasa Diocese, lardin Anglican na Kaduna, Rev. Ali Buba Lamido, wanda ya yaba wa gwamna el-Rufai, a ranar Litinin kan shawarar da ya yanke na rushe cocin.

Ya ce duk wani yunƙuri na rushe ko tsananta wa duk wata Majami’a a jihar Kaduna laifi ne ga Allah da kuma Kiristoci a duk faɗin ƙasar.

“KASUPDA ta rubuta wasika kan umarnin gwamna El-Rufai a gare mu da mu bar harabar majami’ar a cikin kwanaki bakwai, mun kuwa ba da amsa ta hanyoyin da suka fi dacewa tare da kungiyar CAN da sauran kungiyoyin kirista a duk faɗin duniya.”

“Mai makon mu nemi afuwa daga gwamnan, ya dace gwamna ya nemi afuwa daga Ikilisiyar da ma sauran jama’a saboda kunyata kanshi da yake yi da irin wannan umarni da yake gabatarwa.”

Ya bukaci Gwamnan jihar Kaduna da ya daina kunyatar da kansa tare da rushe majami’u a kowane bangare na jihar Kaduna.

‘Yan Fashi da Makami sun Tari Motar ‘Yan Sanda a Kaduna

Wasu da ake zargin su da zama ‘yan fashi da makami sun kaiwa motar ‘yan sanda hari da aska masa wuta a cikin garin Kaduna

Lamarin ya faru ne a dajin Kwanar Labi-Kwaru, kusa da kauyen Udawa a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Wata majiya da ba ta bada rahoton da kuma aka hana bayyana sunan ta, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare bayan wata musayar harbin bindiga da ya afku tsakanin ‘yan sanda tare da wasu da ake zarginsu da zaman ‘yan fashi, a yayin da ‘yan sandan ke akan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Birnin Gwari.

Naija News Hausa ta tuna da cewa ‘yan fashi sun saba da tarin mutane a kan babban hanyar ta Birnin Gwari zuwa Kaduna, inda suke tsananta da kwace mallakar mutane a kan hanayar.

Wata majiya a cikin ‘yan banga da ke tsaro akan hanyoyin sun shaida wa manema labarai da cewa wani dan sanda ya ji rauni a yayin harin, yayin da wasu kuma suka tsere wa rayuwarsu zuwa cikin dajin.

“Su ‘yan sanda na kan tafiya ne a cikin wata farin mota a wani wurin da ake kira Kwaru bayan Kwanar Labi kusa da garin Udawa a lokacin da aka hare su. ‘Yan fashin sun kasance ne da yawarsu, a yayin da suka yi wa dan sanda ɗaya raunuka yayin da sauran suka tsere zuwa daji” inji Majiyar.

“Ko da shike babu wani rai da aka rasa a cikin harin amma ‘yan bindigar sun banka wa motar ‘yan sandan wuta,” in ji shi.

“Na ga lokacin da motar ke konewa saboda ina kan tafiya a wannan ranar a amma dai mun kasa da iya tsayawa ba saboda yankin da lamarin ya faru an wuri ne mai hadari sosai,” in ji shi wani mazaunin yankin da ya ki bayar da sunansa.

Ko da shike a yayin karban rahoton da aka tuntubi Ofisan Hurda da Jama’a na Rundunar Tsaron jihar, ASP Sulaiman Abubakar, ya fada da cewa zai samu cikakken bayani game da harin, a bayan hakan kuma zai bayar da rahoto ga manema labarai, amma dai hakan bai samu ba a lokacin da aka wallafa wannan rahoton.