Labaran Najeriya
Kalli yadda Shugaba Buhari ya bar kauyan Daura zuwa birnin Abuja bayan zaben ranar Asabar
An gano shugaba Muhammadu Buhari a yau misalin karfe 10 na safiya a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya kama hanyar sa da koma birnin Abuja bayan zaben ranar Asabar.
Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Buhari da matarsa Aisha Buhari sun ziyarci kauyan Daura don zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar da ta gabata.
Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Buhari da Aisha matarsa sun jefa kuri’ar su da safiyar ranar Asabar a yayin da aka fara hidimar zaben.
Mun gane da barin shugaban ne a wata bidiyo da Bashir Ahmad ya aika a yanar gizon nishadarwa ta twitter.
Kalli bidiyon;
President @MBuhari leaving his residence, in his hometown Daura, Katsina State for Abuja, after participating in #NigeriaDecides on Saturday. pic.twitter.com/1fG7FDYkfb
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) February 25, 2019
Ko da shike jama’ar Daura na jiran sake marabtan shugaban a ranar Asabar ta gaba don zaben Gwamnonin jiha.