Connect with us

Uncategorized

Mutane 16 sun rasa rayukan su a Jihar Sokoto sakamakon wata hari da ‘yan ta’adda

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwmananatin Jihar Sokoto ta gabatar da wata sabuwar hari da mahara da bindiga suka kai wa Jihar a jiya Litinin, 25 ga Watan Fabrairun, 2019.

Mahara da bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Raba, a Jihar Sokoto. Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Jihar ya bayyana a wata sanarwa da cewa mahara da bindiga sun fada wa kauyan Dalijan, Rakkoni da Kalhu a ranar Litinin da ta gabata.
Ya bayyana da cewa mutane 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan harin, inji shi.
Ya kuma bayyana bakin cikin sa da wannan da kuma isar da gaisuwar ta’aziyya ga jama’ar hukumar Rabah

“Addu’a na shine, Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su sakamakon wannan hari, ya kuma sa sun huta lafiya”

Gwamnan ya kuma karfafa hukumomin tsaron Jihar da cewa su kara kokari da kuzari na ganin cewa sun samar isashen tsari a jihar don tsare rayukan mutane da kuma tattakin arzikin su.

“Kada kuma ku yadda wata rukuni ko ‘yan takaran siyasa su yaudare ku don cika nasu guri kawai ta wurin kisan rayukan mutane” inji Tambuwal.

Mun kuma samu tabbacin labari a Naija News Hausa da cewa ‘yan harin sun kuma sace wata mata mai suna, Hajiya Amina Danmusa, watau matar wani mutumin mai suna Malam Muftahu Yakubu Ciro, a nan garin Danmusa inda ita da mijin ta ke da zama.

Ko da shi ke har yanzu ‘yan harin basu bukaci biyan kudi ba don sake matan, amma ba a gane ko ta ina ne suka tafi da ita ba.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan hari da bindiga sun kashe Insfektan Jami’an ‘yan sanda biyu a Jihar Katsina.