Labaran Najeriya
Zaben2019: Wata yarinza ta fashe da kuka akan murna da cin nasarar Buhari
Ana wata ga wata:
A baya mun ruwaito a Naija News Hausa yadda wani matashi ya tsoma kansa cikin cabi don gabatar da irin murnan sa da cin nasaran Buhari ga zaben 2019.
Da safiyar nan, mun gano bidiyon wata ‘yar mace da ta fashe da hawayen murna a yayin da take bayyana irin na ta murna da farin cikin cewa shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo sun lashe tseren zaben shekarar 2019.
Mun samu bidiyon ne kamar yadda kakakin yada yawun jam’iyyar APC ga lamarin hidimar ralin zaben shugaban kasa, Mista Festus Keyamo (SAN), sa aika bidiyon a shafin yanar gizon twitter.
‘Yar yarinyar ta wallafa bidiyon kanta, yadda ta ke murna da cewa Allah ya sake mayar da shugaba Muhammadu Buhari a kan kujerar mulki.
You don’t buy this with money! Thanks to all the PASSIONATE and COMMITTED supporters of PMB who pulled this through without getting a dime from him, including myself! pic.twitter.com/FD9CdWHlcD
— Festus Keyamo, SAN (@fkeyamo) February 27, 2019
Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Buhari da Osinbajo sun karbi takardan daman komawa ga shugabanci na karin tsawon shekaru hudu gaba, a ranar Laraba 27 ga watan Fabrairu, 2019 daga hannun shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu.