Labaran Najeriya
Zaben 2019: Shugaba Buhari ya halarci Daura kamin zaben ranar Asabar
A ranar Alhamis, 7 ga watan Maris da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci kauyan sa Daura, kamin ranar Asabar da za a gudanar da zaben gwamnoni da ta gidan majalisar jiha.
Mun tuna a Naija News Hausa da cewa hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta gabatar a baya da ranar 9 ga watan Maris a matsayin ranar zaben gwamnoni da gidan majalisar jiha.
Naija News ta gane da shigar shugaba Buhari ne a yayin da ya sauka daga jirgin sama a misalin karfe 6:50 na maraicen ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019.
Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar da darukan sa, hade da masoya sun marabci shugaba Muhammadu Buhari a yayin da ya ke sauka daga cikin jirgin saman.
Naija News ta gane da cewa Hajiya Aisha Buhari da biyo mijin zuwa garin Daura, kuma tana shirin kadamar da zaman liyafa ta godiya ga Mata da matasan kauyan Daura a wannan ziyarar ta su.
Karanta wannan kuma: Masoyin shugaba Muhammadu Buhari da ya sha ruwar kwata, Aliyu ya ce “Ban mutu ba, na saura da rai”