Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sanda a Jihar Kano sun ci karo da Motar Sienna cike da takardun zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Kano sun ci karo da wata motar sienna da aka cika da takardun zabe da aka riga aka dangwala.

Naija News Hausa ta gane ne da hakan a yayin da ‘yan sandan suka kame motar da aka dauki takardun zabe da shi a runfar zaben Makarantan Firamare na Magwam ta karamar hukumar Nassarawa, a Jihar Kano.

An gabatar da cewa an riga an dangwala yatsu ga takardun duka ga ‘yan takaran jam’iyyar APC da ke a Jihar. Jami’an tsaron kuma da suka gane da hakan sai suka ja motar zuwa hedkwatan su.

 

Abdullahi Kiyawa, Kakakin jami’an tsaron ‘yan sandan jihar ya bada tabbacin haka ga manema labarai. Ya kuma bayyana da cewa hukumar su ta kame wadanda suka aiwatar da hakan kuma sun kan bincike akan lamarin.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Ta’adda a Jihar Akwa Ibom sun haska wuta ga ofishin hukumar INEC da ke a Jihar.