Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben Gwamnoni: Shugaba Buhari da Matarsa sun jefa kuri’ar su a Daura

Published

on

at

advertisement

A misalin karfe 8:00 na safiyar yau 9 ga watan Maris 2019,  Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha sun jefa kuri’ar zaben Gwamnoni da ta Gidan Majalisar Jiha a  garin Daura.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari da matarsa sun halarci Daura tun ranar Alhamis da ta gabata gabadin zaben ranar Asabar.

Rahoto ta bayar da cewa Buhari, ya halarci runfar zaben sa da ke a unguwar Sarkin Yara ‘A’ 003 a daidai karfe 8:00 na safiyar. Mallaman zabe yankin sun kuma marabci shugaban a matsayin shi na shugaba da mashi barka da zuwa kamin dada ya jefa kuri’ar sa tare da matar nasa, Aisha.

Shugaban a bayanin shi da manema labarai bayan da ya jefa kuri’ar sa, ya ce “Ina da tabbacin cewa hukumomin tsaro zasu tafiyar da aikin su yadda ya kamata don magance ta’addanci da farmaki wajen hidimar zaben”

Ya kuma kara kafa baki da hirar cewa bai zama abin mamaki ba a gareshi da zargi da kuma karar da jam’iyyar PDP ke yi da shi ba akan zaben shugaban kasa da aka yi a baya ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

“Da man in jiran haka” inji Buhari.

Bayan bada bayani ga manema labarai, shugaban ya bar runfar zaben da matarsa cikin ‘yan kalilan mintoci.