Connect with us

Uncategorized

Jami’an tsaro sun ci nasara da kashe ‘yan Boko Haram 50

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsakanin ranar Jumma’a da Asabar, Rundunar Hukumomin tsaron kasar Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda kimanin mutun hamsin, sun kuma samu kame mutum guda da rai.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a yayin da mai yada labarai ga hukumomin, Col. Timothy Antigha, ya bayyana ga manema labarai a garin Abuja, babban birnin Tarayya.

Timothy a bayanin sa, ya gabatar da cewa an samu nasarar kashe ‘yan ta’addan ne a yayin da hukumomin tsaro daga sashin kasan Chadi, Kamarun, Nijar da ta kasar Najeriya suka hare su daga bangarori daban daban.

“Hukumomin tsaro ta samu ribato wasu kayakin yaki daga ‘yan ta’addan, an kuma lallace wasu sakamakon yadda aka fada masu da wuta” inji shi.

Ya kara da cewa, sun ribato makamai kamar bindigar AK 47 guda 37, wasu mugan bindigogi kuma, babura biyar da motar yaki ukku da dai sauransu.

Ya fada da cewa hukomomin tsaro za ta kara karfafa da kuzari wajen ganin cewa sun dinga cin nasara ga ‘yan ta’addan.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun rusa bam a wata Masallaci a Jihar Borno.