Connect with us

Uncategorized

An Taras da Gawar mutum cikin Rijiya a babban makarantar jami’a ta Jos

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Babban Makarantan Jami’a ta Jos (UNIJOS),  ta bada umarni ga ‘yan makaranta da barin makarantar zuwa gidajen su don guje wa tashin hankali.

Hukumar Jami’ar ta gabatar ne da hakan bayan da suka gane da gawar wani dan makaranta cikin rijiya a unguwar Dutse Uku, nan kewayen makarantar bayan zaben jiha da aka yi.

Wannan abin ya tada hankalin jami’ar a yayin da ‘yan makarantan jami’ar suka fito makil da mamaye kewayan da ikirarin zafin mutuwar matashin da aka iske gawar jikin sa cikin rijiya washe garin jiya Talata, 12 ga watan Maris, 2019.

‘Yan makarantar na zargin cewa matashin ya mutu ne sakamakon zaben gwamnoni da aka gudanar a jihar Jos ranar Asabar da ta gabata. Ko da shike har yanzu ba a iya gane likin yadda abin ya faru ba, ko kuma Jam’iyyar da suka aiwatar da wannan.

An kuma bayyana da cewa ko da shike matashin ya mutu kamin aka gane da cewa yana cikin rijiya, amma abin mamaki, ba wata rauni a jikin sa.

Da jami’an tsaro suka gane da zanga-zanga da ‘yan makarantar jami’an ke yi, sai suka fado wajen don kawar da wata sabon tashin hankali.

A ganin zafin wannan al’amari, hukumar makarantar ta gabatar da cewa ‘yan makaranta su tafi gida har sai an kai ga lafa matsalar.
An kuma bayar da cewa an watsar da jami’an tsaron ‘yan sanda a kewayan a umarnin DSP Mathias Terna Tyopev, Ofisan tsaron yankin, don magance yaduwar tashin hankali a makarantar da kuma kewayan.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gidan Kwanan ‘Yan Makaranta Jami’ar Wudil, a Jihar Kano ta Kame da Wuta