Wata Gidan Sama ta rushe kan 'yan makaranta a Legas | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

Wata Gidan Sama ta rushe kan ‘yan makaranta a Legas

Published

A yau Laraba, 13 ga watan Maris, 2019, Wata Gidan Sama a Jihar Legas ta rushe saman ‘yan makaranta har an rasa rayuka da yawa.

Gidan Saman mai taki ukku da ke a shiyar Ita Faji, a nan birnin Legas ya rushe ne a yau Laraba akan ‘yan makaranta da ke kasar ginin missalin karfe 10 na safiyar yau. Lagos Island, collapsed around 10am.

Ko da shike ba a iya bayyana ko yara nawa ne suka mutu ba a rushewar ginin, amma rahoto ta bayar da cewa a killa yara 10 ne aka samu fitar wa daga ginin a halin yanzu.

“Abin takaici ne wannan rushewar ginin, Iyayen yara na kuka da gaske. Ba na iya tsayawa da kallon wannan lamarin” inji wani da ya samu ganin yadda abin ya faru.

A gabatar a rahoto da cewa an samu fitar da wata yarinya da ta saura da rai kuma an kai ta a Asibiti don kulawa ta gaske.

A halin yanzu, ana kan bincike da neman yadda za a ribato rayukar sauran yaran da ke karkashin ginin, da kuma wadanda wata kila sun mutu nan take.

Idan akwai wata rahoto da ta biyo baya, zamu sanar a wannan shafin..

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gidan Kwanan ‘Yan Makaranta Jami’ar Wudil, a Jihar Kano ta Kame da Wuta

Karanta wannan kuma:  Kalli hotunan ziyarar abokannan Shugaba Buhari tun shekarar 1953 a Daura.

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.