Connect with us

Uncategorized

Gidan Majalisar Dattijai a yau, ta rantsar da Sanata Isaac Alfa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Laraba, 13 ga watan Maris 2019, Gidan Majalisar Dattijai ta rantsar da sabon sanatan Jihar Kogi, Mista Isaac Mohammed Alfa a matsayin sanatan da zai wakilci gabashin Jihar Kogi.

Gidan majalisar ta gabatar da Alfa ne bisa umarnin Kotun kara ta birnin tarayya na cewar Mista Isaac Alfa ne ya dace da kujerar sanatan gabashin Jihar Kogi bayan da aka tsige sanatan da ke wakiltar Jihar a baya.

An gabatar da rantsar da Mista Isaac ni a yayin da gidan majalisar ta kadamar da zaman su a yau, bayan da suka daga zaman su ta ranar Litini don yin ta’aziya ga dan majalisa da ya mutu kwanakin baya.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaban Gidan Majalisar Dattijai, Dakta Bukola Saraki ya gana da Atai Aidoko Ali da tattaunawa akan rantsar da Mista Isaac a matsayin sanatan da zai wakilci gabashin Jihar Kogi.

A baya, Alfa yayi karar Sanata Atai Aidoko Ali da zargin cewa shi ke da damar kujerar da Atai ke a sama bisa zaben firamare da aka gudanar a shekarar 2014 daga Jam’iyyar PDP.

Bayan gwagwarmaya da kararraki, Kotun Kara ta baiwa gidan majalisa umarnin tsige Atai da kuma Sanya Isaac Alfa a matsayin sanatan da zai ci gaba da wakilcin gabashin Jihar.

Karanta wannan kuma: Aikin mu na kare yancin Al’umma ne, inji fadin ‘yan sandan Jihar Kano