Uncategorized
Kimanin mutane 22 suka mutu a wata harin Mahara da bindiga a Birnin Gwari, Kaduna
An gabatar da wata harin da mahara da bindiga suka kai wa Layin Maigwari da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, inda ‘yan harin suka kashe rayuka 22.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 55, sun kuma kubutar da rayuka 760 a Jihar Zamfara
Wani mazaunin garin Birnin Gwari ya bayar ga manema labarai da cewa mugun harin ya faru ne missalin karfe 7:00 na safiyar ranar Talata, 12 ga Watan Maris da ta gabata, a yayin da maharan suka fada wa garin da harbe-harben bindiga ko ta ina.
Bincike ya nuna da cewa kauyan, inda ‘yan harin suka aiwatar da harin na da nisar minti ashirin (20) ne kawai da cikin garin Birnin Gwari ta hanyar Funtua.
An kuma bayyana ga manema labarai da cewa harbe-harben ya dauki tsawon awa daya da barin mutane ashirin da biyu a kasa, da kuma rauna mutane da yawa a yayin da mutanen garin ke kokarin guje wa harsasu.
“A lokacin da ‘yan harin ke batun wuce wa bayan harbe-harbe da suka wa mutane, ‘yan banga yankin su fada masu a gaba da musayar wuta. Amma dai ‘yan harin sun samu kashe mutum biyu daga cikin ‘yan bangan” inji mazaunin wajen a bayanin sa da manema labarai.
A lokacin da aka kira kakakin yada yawun jami’an tsaron ‘yan sanda yankin, DSP Yakubu, ya bayar da cewa yana kan tafiya amma idan ya sauka sai mayar da kira. Amma har lokacin da aka bayar da rahoton nan, ba a samu karban bayani daga bakin sa ba.