Connect with us

Uncategorized

Kash: An gunce hannun wata tsohuwa a Jihar Kwara

Published

on

at

advertisement

Abin takaici, wani mai suna Lukman ya gunce hannun wata mata mai shekaru 60 a yankin Omu-Aran ta Jihar Kwara, a ranar Asabar da ta gabata.

An bayyana ga menama labarai da cewa abin ya faru ne daren ranar Asabar da ta wuce, a yayin da Lukman ya gunce wa Muibat Abifarin hannu bayan wata gardama da ta tashi tsakanin Abeeb Abifarin, yaron tsohuwar da Lukman akan zargin cewa Lukman ya gasa wata akuya.

An kara bayyana da cewa Lukman na da alamun haukacewa, a yayin da aka gane da cewa ya hari wasu mutane biyu da suke zama cikin gida guda a Orolodo, nan kusa da fadar sarkin Omu-Aran ta Jihar Kwara.

An gabatar da cewa matar, an kai Muibat a asibiti a gaggauce don karban kulawa ta gaske. sauran mutane biyu kuma da Lukman yayi wa rauni a na a nan Asibitin Tarayya ta Omo-Aran don samun kulawa ta kwarai.

“Muibat na samun isasshen kulawa, amma ba a bar kowa ya shiga ganin ta ba, sai har ta samu karin sauki a nan cikin asibitin da ta ke” inji manema labarai da ya ziyarci wajen.

“Abin ya faru ne missalin karfe 10 na daren ranar Asabar lokacin da kowa a gidan ke kokarin shiga barci. Gardama ya tashi ne tsakanin Lukman da yaya na Abeeb akan wata Akuya da Lukman ya soye. Daga nan gardaman tayi zafi har Lukman ya hari Abeeb da kokarin ya sare shi da Adda”

“Ana cikin hakan ne sai ga tsohuwar mu ta fito daga dakin barci da ta ji kuwace-kuwace. A kokarin ta na kare Abeeb daga harin Lukma, shikenan sai ya hari maman mu da addan; Yana kokarin sare ta akai ke nan sai ta tara hannun ta, kawai sai Lukman ya gunce mata hannu” inji Azeez, daya daga cikin yaran tsohuwar da Lukman ya gunce wa hannu.

Tsohon Lukman, ko da shike yayi rokon cewa kada a bayyana sunan sa, ya fada da cewa “Hankali na ya tashi kwarai da gaske lokacin da na ga yanayin. “Ina a gidana sai ga kira da cewa Lukman ya aiwatar da wannan mugun abin”

“Na tsorata kwarai da gaske da na isa wajen, na kuma ga yadda yanayin ya kasance”

“Lukman ya kasance a gida na wuni daya kamin abin ya faru. Amma abin mamaki shine, bai nuna wata alaman mutun mai kulle da wata mugun shiri ba” inji babban Lukman a lokacin da yake bayani da manema labarai a nan Asibitin da ake bada kulawa ga malama Muibat.

An bayar da cewa jami’an tsaron shiyar sun kame Lukman, sun kuma sa shi a kulle nan ofishin su.

“Ana kan karin bincike a kan lamarin” inji daya daga cikin jami’an tsaron da ke karar Lukman.