Uncategorized
INEC ta gabatar da ranar da za a kamala zaben Jihar Adamawa
Hukumar Gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) ta gabatar a yau da ranar da zata kamala zaben Jihar Adamawa.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Kotun Koli ta bada dama ga Hukumar INEC don ci gaba da hidimar zaben Jihar Adamawa.
Hukumar ta gabatar da ranar Alhamis, 28 ga watan Maris 2019 don karshe zaben Jihar Adamawa. Wannan gidan labarin ta gane da hakan ne a wata sanarwa da Kwamishanan Hidimar Zaben Jihar, Kassim Gaidam ya bayar a yau, nan garin Yola bayan da Kotun koli ta janye karar da ake akan zaben a baya.
“Kotu ta riga ta janye karar da ake da kuma umurnin da ta bayar a baya na dakatar da hidimar zaben. Hukumar mu na da daman ci gaba da kadamar da zaben Jihar Adamawa a halin yanzu, kamar yadda aka yi a sauran Jihohin kasar” inji Kassim.
“Ganin wannan, Hukumar ta gana da jami’an tsaro, an kuma amince da gudanar da zaben ranar 28 ga watan Maris 2019, watau Alhamis ta gaba.” inji shi.