Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya kama hanyar zuwa kasar Senegal

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Litini, 1 ga watan Afrilu, Shugaba Muhammadu Buhari hade da wasu manyan shugabannai a kasar sun shiga jirgin sama zuwa Dakar, kasar Senegal.

Naija News Hausa ta gane da cewa ziyarar shugaba Muhammadu Buhari a Dakar ya kama ne don hidimar nadin sabon shugaban kasar Senegal, Macky Sall.

An gabatar ne da wannan rahoton daga bakin kakakin yada yawun shugaban kasar Najeriya, Femi Adesina, a wata sanarwa da aka bayar a yau Litini.

Zuwar shugaba Buhari ya kama ne kamar dole bisa ga wata wasikar gayyata da aka aika wa shugaban a matsayin shi na ciyaman na kungiyar ECOWAS ta tarayyar kasa.

Sanarwan ta nuna da cewa Gwamnonin kasar Najeriya kamar, Gwamna Mohammed Abubakar, Nasir El-Rufai da Tanko Al-Makura zasu mara wa shugaba Buhari baya ga ziyarar.

Ziyarar kuma zai halarci wasu manyan shugabannan kasar Najeriya, kamar su; Ministan Ayukan Kasar Waje Geoffrey Onyeama, Mai bada Shawara ga Lamarin tsaron kasa, Maj-Gen Babagana Monguno (rtd); da kuma Anbasada Ahmed Rufai hade da wasu manya da ba a gabatar da sunayan su ba.

Karanta wannan kuma: Kotu ta saka wani gidan jaru na tsawon shekaru 10 da zargin kisan kai