Connect with us

Uncategorized

Sojoji Najeriya sun ci karo da inda ake Kirar Bindigogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hedkwatan Rundunar Sojojin Najeriya ta ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS), a wata zagayen bincike da suka yi a Jihar Nasarawa, Taraba da Jihar Benue, sun gabatar da cewa sun ci karo da wasu mutane biyu da ake zargin su da kirar bindigogi a karamar hukumar Logo ta Jihar Benue.

Naija News Hausa ta samu gane da wannan labarin ne kamar yadda Maj-Gen Adeyemi Yekini, Kwamandan Rundunar Sojojin OPWS ya gabatar a garin Makurdi ga menama labarai a ranar Litini da ta gabata.

Ya ce bayyana da cewa sun kame mutane biyun da aka iske da kirar bindigogi da rashin bin dokar kasa.

“Wani ne yayi mana kirar kula game da lamarin. Bincike da gano Makeran kuma ya dauke mu tsawon makonnai hudu kamin dada muka gane ainihin wajen da ake kirar, da kuma kame masu kirar” inji Janar Yekini.

“Kame makerar bindigogin bai zama mana da sauki ba ko kadan” inji Kwamandan wata yanki na Rundunar Sojojin OPWS da ke a shiyar, Capt. Samuel Okinahi.

Ya bayyana da cewa sojojin sun ribato makamai iri-irin a inda ake kirar. Ya kuma bayyana da cewa masu kirar sun gabatar da cewa suna da masu sayan makaman a cikin Jihar Benue da Taraba.

A bayanin sa, ya bayyana da cewa rundunar Sojojin sun yi nasarar hakan ne tun ranar 24 ga watan Maris 2019 da ta gabata.

Daya daga cikin masu kirar ya bayyana ga manema labarai da cewa ya karancin Injiniya ne na Fasaha da hanayar Sadarwa a Makarantar Jami’a ta Mauritania (Turai), har ga tsawon shekaru biyar, inji shi.

Ya kara da cewa a can ne ya karanci yadda ake kirar Makamai. “tun da na dawo kasar Najeriya ban samu wata aikin kwarai ba a kasar, sa’anan ga matsalar Mayu a kauyan mu.”

“Duk kokari na da samun aiki mai kyau tun lokacin da na dawo kasar Najeriya a banza ce. Musanman akan matsalar Mayu da ke a kauyan mu” inji shi.

“Da na gane da cewa na yi barnan kudi da dama ba tare da samun wata riba ko ci gaba ba a kasar, sai na dauki wannan dama, musanman ganin irin halin matsalar yaki da tsaro da ke yankin mu. Daga nan sai na fara kirar makamai don taimaka wa rayuwa na”

A bayanin sa, ya kan sayar da Bindiga AK47 kusan naira dubu N350, 000 zuwa dubu N400, 000. Ita kuma karamar bindiga da aka fi sani da suna Fistu ta kan kai naira dubu N150,000.

“Na kai tsawon shekaru biyu da fara wannan sana’ar, ina kuma da masu sayar bindigogi da makamai a Jihar Benue da Taraba” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Mahara da Bindiga sun kai wata sabuwar hari a kauyuka biyu ta karamar hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ranar Lahadi da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa kusan mutane goma sha shidda ne ‘yan harin suka kashe a kauyan Kursasa da Kurya a nan karamar hukumar Shinkafi, Zamfara.