Connect with us

Uncategorized

Motar Tirela ya kihe kasa da barin wata Macce mai ciki da wasu da raunuka a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata Motar Tirela da ke dauke da ‘Ya’yan itãcen marmari da kayan lambu ya Kihe da raunana mutane hade da Macce mai ciki a garin Minna, babban birnin Jihar Neja.

An bayyana da cewa hakan ya faru ne a garin Minna a bayan da motar ta tashi ci gaba da tafiyar ta na zuwa Jihar Legas dauke da ‘Ya’yan itãcen marmari da kayan lambu da ta dauko daga Jihar Filatu.

Wani da ya gana da yadda hadarin ya faru, ya bayyana ga manema labarai da cewa wata mata da ke dauke da ciki ta samu rauni daga hadarin motar a yayin da take kokarin ketara kan babban hanyar da ke a wajen, sai kawai buhun kayan lambu ya fado mata.

Ya kuma bayyana da cewa an kai matan da sauran mutanen da suka samu raunuka a asibitin don basu isashen kulawa ta gaske.

“Motar ta kihe ne a sakamakon ruwan sama da aka yi tsakar rana a garin Minna. Ba na cikin mugun gudu, na kuma yi murna da cewa ba wanda ya mutu a hadarin” inji Mallam Isah Kuta, direban Motar Tirelan da ta kihe.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mutane Goma Sha Ukku (13) sun mutu a wata Mumunar Hadarin Mota a tsakanin hanyar Jihar Bauchi zuwa Gombe.