Connect with us

Uncategorized

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto sun kame ‘yan ta’dda da suka gunce wa wani hannu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 9 ga watan Afrilu, Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Sokoto sun gabatar da kame wasu ‘yan ta’adda da suka gunce wa wani mutumi hannayan sa biyu a Jihar Sokoto.

Ofisan yada yawun Hukumar ‘yan sandan Jihar, Sadiq Abubakar Mohammed ya bada tabbacin kame ‘yan ta’addan a wata bayani da ya bayar ga gidan Talabijin Labarai ta TVC a kan wayan Salula.

Ya bayyana da cewa lallai gaskiya hakan kuma hukumar na kan kara bincike da lamarin. “Muna kan bincike akan al’amarin, zamu kuma sanar da al’umma da karin bayani akan binciken mu a nan gaba” inji shi.

‘Yan ta’addan sun gunce wa Habibu Abubakar, wani matashi hannayan sa biyu ne a ranar Lahadi da ta gabata. Ko da shike ba a bayyana dalilin hakan ba, amma dai an riga an kai Habibu asibiti tun ranar Lahadi don yi masa kulawa ta gaske.

Wani da ya samu ganin yadda abin ya faru, ya bayar ga manema labarai da cewa ‘yan ta’addan sun hari Habibu ne a gidansa da mugayan makamai a shiyar Nakasari da ke a karamar hukumar Kuducin Sokoto, missalin karfe 2:00am na safiyar ranar Lahadi da ta gabata da barin shi da guntayan hannu.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa wani mutumi da ake dubin shi da tabuwar kwakwalwa, ya sare wani dan Sanda da Adda a Jihar Kwara.