Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Manyan Shugabannan tsaron kasa

Published

on

at

Naija News Hausa ta karbi rahoto da ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari a yau Alhamis, 11 ga watan Afrilu 2019, na zaman kofa kulle don tattaunawa da manyan shugabannan hukumomin tsaron kasar.

Zaman ta fara ne missalin karfe goma sha daya (11:00am) na safiyar yau a nan Fadar Shugaban Kasa ta Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

Ko da shike ba a bayyana dalilin zaman gaugawan ba, amma muna hangen cewa zaman ba zai wuce akan matsalar hare-hare da kashe-kashen rayuka da ke gudana a kasar ba. Musanman a Arewacin kasar Najeriya.

Zamu sanar da sakamakon ganawar jin kadan da nan a shafin mu na Hausa.NaijaNews.Com

Karanta wannan kuma: Shahararrar ‘yar shirin fim a Kannywood, Hadiza Gabon ta sake fada da wata a fagen hadin fim.