Connect with us

Uncategorized

Muna a Shirya don Kare Nasarar Ganduje a Jihar Kano – APC

Published

on

at

advertisement

Jam’iyyar APC ta Jihar Kano sun gabatar da ranar Laraba da ta gabata da cewa suna a shirye don kare nasarar Abdullahi Ganduje, da dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kano daga Jam’iyyar APC yayi a tseren zaben 2019 da aka kamala makonnan da suka gabata a Jihar.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta Jihar Kano ta baiwa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da sabbin ‘yan gidan Majalisu 27 takardan komawa ga kujerar shugabanci.

Jam’iyyar APC sun gabatar a bakin Mista Ma’aruf Mohammed-Yakasai, mamba da kuma kakakin yada yawun kungiyar rukunin Jam’iyyar APC, a ranar Laraba da ta gabata da cewa suna a shirye don kare cin nasara da dan takaran su yayi ga zaben ranar 23 ga watan Maris da ta gabata.

Yakasai ya bayyana hakan ne ga manema labarai a wata ganawa da suka yi a Jihar Kano ranar Laraba da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa Yakasai ya fadi wannan ne bisa bada damar da Kotun Kara ta yi ga Jam’iyyar PDP ta Jihar Kano don kadamar da bincike akan kayakin da Hukumar INEC tayi amfani da su a wajen hidimar zaben Jihar Kano da aka kamala.

“A matsayi na na mamban wannan rukuni ta mu da kuma matsayina na kakakin yada yawun rukunin, mun karbi umarni daga Kotu na bayar da dama ga Jam’iyyar PDP don yin bincike akan kayakin da aka yi amfani da su a zaben Jihar Kano”

“Kotun kuwa ta bamu Foto Kwafin takardan, zamu kuma kasance a wajen don tabbatar da cewa an tafiyar da hidimar binciken a hanyar da ta dace” inji shi.

A bayanin Yakasai, dan takaran Jam’iyyar PDP ga tseren zaben 2019, Abba Kabir-Yusuf bai da wata muhinman zargi ko shaidu da zai bayar don nuna rashin amincewa da nasarar Ganduje ga hidimar zaben watan Maris a Jihar.