Uncategorized
Zaben 2019: Da Makirci Ganduje ya lashe zaben Jihar Kano – Abba Kabir
Dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kano daga Jam’iyyar PDP, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da cewa da Makirci ne Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya lashe zaben Jihar Kano.
Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta bayar da takardan komawa ga kujerar shugabancin Jihar Kano ga Abdullahi Ganduje, dan takaran Gwamna daga Jam’iyyar APC.
Abba Kabir ya gabatar da zargin Ganduje da Makirci ne a ranar Laraba da ta gabata, a wata sanarwa da aka bayar daga bakin kakakin yada yawun sa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Sanarwan na kamar haka, “Dakta Abdullahi Umar Ganduje, dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kano daga Jam’iyyar APC ya lashe zaben Jihar ne akan Makirci da halin cin hanci da rashawa.
“Na gane da cewa Ganduje bai cikin hankalin sa da shiga rawar murna bisa sakamakon makircin zaben da aka yi a Jihar Kano a ranar 23 ga watan Maris da ya gabata a shekarar 2019.” inji Abba.
Abba ya kara da cewa zaben Jihar ya kasance ne da makirci, cin hanci da rashawa, tsananci da kuma yaudara.
Karanta wannan kuma: Kotun Kara ta bayar da dama ga PDP don binciken kayan hidimar zaben Jihar Kano