Connect with us

Uncategorized

Gobarar wuta ya ratsa Shaguna Shidda a Birnin Kebbi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta gane da wata gobarar wuta da ya kone Shaguna Shidda (6) a Birnin Kebbi ranar Jumma’a da ta gabata.

Bisa bincike da ganewar manema labarai, an bayyana da cewa shagunan da suka kone a daren ranar Jumma’a da ta wuce na cike ne da Magunan Feshi da kayakin Noma a cikin ta.

Daya daga cikin masu gadin kasuwar, Malam Aminu Shehu, ya bayar ga manema labarai da cewa har yanzu ba su iya sun gane da sanadiyar kamun wutar ba. Amma da cewa Hukumar Yaki da Gobarar Wuta (Fire Service) ne suka taimaka da kashe yaduwar wutan cikin kasuwar.

“A yayin da ni ke cikin aikin gadin shagunan da ke cikin kasuwar, sai na hango hayakin wuta daga sama missalin karfe 10:00 na dare, Da ganin hakan sai na haska toci na don gane inda hayakin ke tasowa. Ko da zan tada kai sai na gane da cewa wuta ya kame daya daga cikin shagunan ne da nike tsaro”

“Anan take sai na yi kirar taimako. amm bamu iya gane ko menene sanadiyar gobarar ba” inji Shehu.

“Mun rasa kudi kimanin Miliyoyi da dama sakamakon wannan  gobarar wutan.” inji bayanin Mallam Muhammad Lawal, mai shugabancin sha’anin saye-da-sayarwar shagon Saro Agro Science Nig Ltd, ga manema labarai

Lawal ya kara da cewa “Lallai a haka ba zani iya bayyana ko nawa ne muka rasa ga wannan mugun gobarar ba. Amma zamu yi lissafin kayakin da uka kone a baya ko zamu iya kimanta abin da muka rasa” inji shi.

Ko da shike Hukumar Jami’an Tsaro da Hukumar Yaki da Gobarar wuta basu bada wata bayani ba tukunna game da gobarar. Amma Mista Ajala Olusoji, daya daga masu saye-da-sayarwa cikin kasuwar ya bayyana da cewa suna cikin kokarin ganin cewa sun ribato wasu kayaki daga cikin gobarar da basu gama lallacewa ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gobarar Wuta ya Kone Shaguna Takwas a Jihar Katsina