Labaran Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Kungiyar FEC a birnin Abuja
A yau Laraba, 17 ga watan Afrilu 2019, shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Kungiyar Manyan Tarayyar kasa (FEC) a nan fadar shugaban kasa ta Abuja, babban birnin Tarayya.
Ko da shike zaman tattaunawar ya fara ne tun missalin karfe goma sha daya na safiyar yau, amma har yanzu ba a gabatar ko kuma bayyana abin da ake ganawa akai ba.
Bisa bayanin manema labarai, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa wajen tattaunawar ne missalin karfe 10:59 na safiya. An kuma bayyana da cewa mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo bai samu kasancewa wajen tattaunawar ba akan wasu dalilai.
Taron ya halarci Manyan shugabannai a kasar, kamar su Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Babban Shugaban Tsaro, Abba Kyari, Mai bada Shawarwari ga Tsaron Tarayya, Babagana Monguno hade da Ministocin kasar guda Ashirin da daya (21).
Zamu sanar da duk wata hira da ya biyo baya akan tattaunawar shugaba Buhari da kungiyar FEC a wannan layi tamu na Hausa.NaijaNews.Com