Connect with us

Uncategorized

Abin Takaici, An gano wani Jariri a Cikin Rijiya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da gane wani dan Jariri da Maman tayi watsi da shi bayan haifuwa.

Bisa bayanin Jami’an tsaro, an ajiye jaririn ne a cikin wata rijiya da ba a amfani da shi, da ke a wata shiyya na karamar hukumar Kaugama.

Naija News Hausa ta samun tabbacin hakan ne bisa wata gabatarwa da hukumar ta bayar daga bakin SP Abdu Jinjiri, Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar, a ranar Litinin da ta wuce ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN).

“Wakilin garin Kuka-Kwance, da ke da shekaru 40 da haifuwa, da suna AbdulAziz Lawan ne ya kawo jaririn a Ofishin Jami’an Tsaro tun a ranar 20 ga watan Afrilu missalin karfe Hudu na Maraice” inji SP Abdu.

“Ya bayyana da cewa an ajiye jaririn ne a cikin rijiya bayan haifuwarsa aka kuma yi watsi da shi a wurin” inji shi.

Lawan ya kara da gabatar da cewa jaririn na cikin isashen lafiyar jiki, bisa binciken asibiti a yayin da aka kai shi a can don kulawa ta gaske.

A halin yanzu ba a iya gane ko wa cece ta aikatar da hakan ba, amma kan bincike don hakan da kuma gane dalili.

SP Abdu ya bayyana da cewa Hukumar su na kan bincike kan al’amarin, idan akwai karin biyani da ya biyo, zamu sanar a layin mu ta Hausa.NaijaNews.Com

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar ‘yan tsaron Jiha ta (JTF) sun gano wani jariri kulle a cikin leda a bayar Asibitin Badarawa. ta Jihar Kaduna.

An bayyana da cewa an cinma jaririn ne cikin wata bakar leda da maman ta ajiye shi da kai waje, da kuma wata sako da ta wallafa don duk wanda ya samu cintar yaron.