Uncategorized
Wata Macce ta kashe Mijinta da hadin kan Yaron su, a Jihar Neja
Hukumar Jami’an tsaron Jihar Neja sun kame wata Macce mai shekaru 50 da haifuwa da zargin kisan Kai.
Wata Mata mai suna Hafsat Aliyu da yaron ta mai suna Babangida Usman, sun yiwa Maigidan da ake kira Ali Haruna duuka har ga mutuwa.
Naija News Hausa ta gane da cewa wannan al’amarin ya faru ne tun ranar 13 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 a shiyar Makarantar Firamare na Shango da ke a karamar hukumar Chanchaga, ta Jihar Neja.
An bayyana ga manema labarai da cewa Usman da Maman shi sun hari mutumin ne da bugu a zargin cewa Maigidan a kullum bugun matanshi ya ke.
“Na yi kokarin ne kawai in k’are tsohuwa na daga hannun Baba na. ban yi tsanmanin abin zai kai ga hakan ba” inji Usman a yayin da ake neman shi da bayani.
“Tsohuwa na ba a k’are take ba inda tana ita kade da Baba na saboda irin halin fushi da zafin zuciya da yake da shi. A koyaushe sai ka ji su da wata matsala har ga fada. Ban san da cewa abin zai kai ga hakan ba, ni dai kokarin k’are mamana ne kawai na yi.” inji shi.
Kakakin yada yawun ‘Yan Sandan yankin, Mohammad Abubakar, ya bada tabbacin hakan da cewa lallai Usman da Hafsat sun amince da zargin kisan kai da ake da su.
Ko da shike dai an kai mutumin a Asibitin Ibrahim Badamasi Babangida da ke shiyar, amma ba a samu ceton ran shi ba.
A halin yanzu ana kan karar Usman da Maman sa, za a kai su a gaban Kotu don hukunci bisa doka.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar ‘yan sandan Jihar Kano sun sanar da kame wata Macce da ta dauki matakin sa guba cikin abincin mijin ta.
Matar da ke da tsawon shekaru 15 ga haifuwa, Hassana Lawan daga kauyan Bechi da ke a karamar hukumar Kumbotso ta saka guba cikin abincin mijinta, Sale Abubakar da ke da shekaru 33 haifuwa.