Connect with us

Uncategorized

Walwashi a Jihar Gombe a yayin da Gwamna Dankwambo ya janye dokar ƙuntatawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Naija News Hausa, Labaran Siyasa, Labaran Najeriya a Yau, Jihar Gombe

Al’ummar Jihar Gombe sun samu saukin lamari a yayin da Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya dakatar da dokar ƙuntatawa na awowi goma sha biyar da aka sanar a Jihar a baya.

Naija News Hausa na da sanin cewa Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara dokar ƙuntatawar ne daga ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu zuwa ranar Lahadi 28 ga watan Afrilu don magance da dakatar da yanayin matsalar hare-hare da kashe-kashen rayuka da ke aukuwa a Jihar.

Dankwambo ya gabatar da dokar ƙuntatawar ne musanman don kisan wasu ‘yan Boys’ Brigade (wata rukunin ‘yan Addini Kirista) takwas da hukumar ‘Civil Defence (NSCDC) suka kashe bayan Sujada a gaban Ikilisiya makon da ta gabata, wanda ya jawo farmaki tsakanin mutanen Jihar.

Sakataren Jihar Gombe, James Pisagih, a wata sanarwa da aka bayar a yau ya bayyana da cewa Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya bada umarnin janye dokar ƙuntatawar zuwa karfe 10 na dare.

Ga bayanin a kasa kamar haka;

“Gwamna Dankwambo ya bayar da umarni ga hukumomin tsaron Jihar Gombe da janye dokar ƙuntatawa zuwa karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safiya har sai komai ya lafa a Jihar.” inji Pisagih.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya gabatar da dokar ƙuntatawar a Jihar don lafa matsalar hari da ake kai-da-kai a Jihar Kaduna.