Connect with us

Labaran siyasa

Kannywood: Muna da kudurin Fita takaran zabe nan gaba – inji Ali Nuhu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Labaran Hausa, Labaran Najeriya, Kannywood, Ali Nuhu

Daya daga cikin ‘yan shirin fina-finai a Kannywood, Kwararre da Fitacce, Jarumi Ali Nuhu ya rattaba baki ga zancen hidimar takaran zabe a kasar Najeriya.

Naija News Hausa ta samu wannan rahoton ne bisa wata ganawa da Jarumin yayi na tattaunawa da gidan labaran BBC.

“Wasu jaruman fina-finan Hausa na da kudurin fita da tsayawa takaran zabe a kasar Najeriya nan gaba.” inji Ali.

Wannan itace bayanin Ali Nuhu a ganawar shi da manema labaran BBC a wata zaman tattaunawa ta musamman da suka yi da shi.

Jarumin ya ci gaba da bayyana da cewa a halin yanzun ma, fita takara da daya daga cikin gurin ‘yan shirin fina-finai a kannywood. “A gaba ma yanzu, yana daga cikin irin kudurin da muke da shi, na ganin cewa wasu daga cikinmu sun fito a 2023 don tsayawa ga takara,”

“Ai jarumai irinsu Abba El-Mustapha da Nura Hussaini duk sun taba tsayawa takara a zabukan Najeriya” inji Ali Nuhu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rikici ta barke tsakanin ‘yan shirin Fina-fina a kannywood akan wata kudi da ‘yan siyasa suka bayar a garesu.

Da aka yi tugumar Ali Nuhu da tambaya, shi cikin raha ko wata rana za a ga fasta dauke da hoton Ali Nuhu yana takaran shugaban kasar Najeriya? kawai jarumin sai ya kyalkyale da dariya da cewa, “Ah haba! Gaba daya?”

An kara bukatar shi da bayyana sunayen wadanda ke da muradin fita zabe a Kannywood, sai ya ce “Lallai ba zan iya fadar sunayen su ba a halin yanzu, dalili kuwa itace, ana kan tattaunawa da shiri akan hakan”.