Connect with us

Labaran Najeriya

Jami’an tsaron Katsina sun kame wadanda ake zargi da sace Magajin Garin Daura

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00
Labaran Najeriya a Yau

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa Hukumar Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Katsina sun bayyana da cewa sun yi nasara da kame mutanen da ake zargi da sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar.

Mun sanar a wannan gidan labarai ta mu da safiyar yau da cewa an sace Alhaji Musa, Magajin Daura a gidan sa.

Sai ga shi hukumar tsaron jihar na sanar a yanzu da cewa lallai sun ci nasara da gane wadanda suka sace Alhaji Musa.

Ko da shike mun sanar a baya da cewa Magajin Garin Daura suruki ne ga shugaba Muhammadu Buhari, amma an kara bayyanawa da cewa lallai ba ainihin surukin shi ba ne kamar yadda aka bayar, amma dai surukin ne ga Colonel Mohammed Abubakar, ADC da shugaba Muhammadu Buhari a lamarin tsaro.

Naija News ta gane da cewa Jami’an tsaro sun hari shiyar ne da bincike da neman liki har suka kai ga hadewa da ‘yan harin da suka sace Magajin Garin Daura.

Wannan nasarar, kuzari ne da hadin kan Kwamishanan ‘Yan Sandan Jihar Katsina, CP Sanusi Buba, hade da jami’an tsaro da suka hari ‘yan ta’addan.

An bayyana ne da cewa Jami’an tsaro sun yi ganawar wuta da ‘yan harin harma daya daga cikin jami’an tsaron yayi mugun raunin harbin bindiga sakamakon harbin da maharan suka yi masa a ganawar wutan. Ko da shike an riga an kai shi a asibitin Federal Medical Center ta Katsina don bashi kulawa ta kwarai.

A halin yanzu ba a bayyana lafiyar jikin Alhaji Musa ba bayan sace shi da aka yi, amma dai bisa wannan rahoton, akwai alamun cewa an iske shi cikin koshin lafiya.