Connect with us

Uncategorized

Karanta yadda Kocin Liverpool ya rattaba wa Messi bayan wasan su da Barcelona

Published

on

at

Naija News Hausa na da sanin cewa wasan kwallon kafa na UEFA Champions League tsakanin Barcelona da Liverpool da aka yi a daren ranar Laraba, 1 ga watan Mayu ya karshe ne 3 – 0, a yayin da Lionel Messi ya lashe ragar Liverpool da gwalagwalai 2, shi kuma tsohon dan wasan Liverpool na da, Suarez ya jefa gwal 1 a ragar tsohon kulob na shi.

Ko da shike dai, ‘yan wasan kwallon Liverpool sun taka rawar gani a wasan, amma basu da sa’ar gwal. Haka kuma ga ‘yan wasan Barcelona, su ma sun yi nasu kokarin, musanman ma sun dace da jefa gwalagwalai 3 ga ragar Liverpool a Filin kwallon wasan Camp Nou.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, bayan da aka kamala wasan, manema labaran wasan kwallo sun bincike shi da bayani, ya kuma bayyana a cikin bayanin sa da cewa “Lallai wasar bai zama da mamaki ba a gareni, Messi shahararren dan wasa kwallo ne a dukan duniya, kowa ya san dashi, ya kuma nuna hakan a hadewar mu da su”

Kalli bayanin a Turance a layin Twitter;

“Bamu iya mun dakatar ko hana shi cin Firikik da ya buga ba, ba nan kade ba, ya nuna da cewa lallai shi kwararre ne a wasar. Mun yi iya kokarin mu da iyawarmu, amma wasar ta kare yada ta kare.” inji Klopp.

KARANTA WANNAN KUMA: Yafi Kyau da dacewa a Aurar da ‘ya Macce ko ‘Da Namiji da kankanin Shekaru – inji Akashat Ny’mat