Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Najeriya sun Dakatar da Aikin Kabu-Kabu a Arewacin Najeriya, Kalli Jihohin da abin ya Shafa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata ta sanar da dakatar da ‘yan Kabu-kabu da ake cewa (Okada) daga aiki a wasu wurare a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Sojojin sun bayyana da cewa sun yi hakan ne don kawo karshen tashin hankali, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci a Jihohin Kasar.

Rukunin Rundunar Sojojin HARBIN KUNAMA ne suka gabatar da wannan dokar dakatar da ‘ya Kabu-Kabu daga aiki a yankunan Jihar Kaduna, Kano, Kebbi, Katsina, Sokoto, Zamfara da Jihar Neja, inda ake fuskantan ta’addanci da sace sacen mutane.

Wannan dokar a musamman ya shafi yankunan da ta’addanci ke aukuwa ne a Jihohin kasar da aka lisafta a sama, inda ‘yan hari da ‘yan ta’adda ke ɓoyewa.

Rundunar Sojojin sun kuma yi kira ga gwamnonin jihohin da su hada Sojan Rukunin Sojoji wajen tabbatar da ganin cewa an bi wannan umarnin, don sake mayar da zaman lafiya da tsari a kasar.

Naija News Hausa ta gane da wannan sanarwan ne da aka bayar ga manema labarai ta bakin mai magana da yawun hukumar Jami’an tsaro, Colonel Sagir Musa.

Sagir ya ce, “Rundunar Sojojin Najeriya da tsawon lokaci sun lura da amfani da yadda masu linzami, masu sace-sacen mutane, masu aikata laifuka da ya shafi ta’addanci ke haɗa kansu masu Babura don taimakawa wajen ci gaba da aikata mugan ayuka a Jihohin kasar”

“Wannan ya sanar da shawarar da umurni don hana amfani da motoci a cikin yanki musamman a cikin gandun daji inda ‘yan fashi, masu aikata laifuka da masu sace-sacen suka sacewa da kuma duk inda dakarun ke gudanar da aiki tare da sauran jami’an tsaro.

“Ganin hakan ne ya jawo matakin da Rundunar Sojoji ta dauka na dakatar da ayukan Kabu-Kabu a wadannan yankunan, sai har komai ya lafa”

“Duk da yake wannan zai iya haifar da wasu matsaloli ga wasu ‘yan ƙasa masu zaman kansu, watau masu bin doka. Amma ya zama dole a yi hakan don tabbatar da tsari a kasar” inji Col. Sagir.

KARANTA WANNAN KUMA: ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Mutum Ukku daga gida guda da zargin Kisa