Connect with us

Labaran Najeriya

#Ramadan: Kuyi Addu’a don Ci Gaban Kasar Najeriya – Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da gaisuwa ga ‘yan Najeriya, musanman ga Musulmai, yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Naija News Hausa ta samu tabbacin gaisuwar shugaba Buhari ne bisa wata sanarwan da Babban Mataimakin shugaban a lamarin sadarwa, Mista Garba Shehu ya bayar a ranar Lahadi da ta gabata.

Wannan sanarwan ya laso baya ne bisa sanarwan da Sarkin Musulmai yayi na ganin watan Ramadan a Sokoto da kuma sanar da cewa za a fara Azumi yau Litini, 6 ga watan Mayu a shekara ta 2019.

A cikin sanarwan, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga ci gaba da zaman lafiyar kasar Najeriya.

“Addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, Addini da ke goyon bayan dabi’u na juriya da haɗin kai tare, Addinin da bai bada daman ƙiyayya ba da tashin hankali” inji Buhari.

Saboda haka, Shugaban ya bukaci Musulmai da yin amfani da lokacin Azumin nan don gina dangantaka ta aminci, da kuma jituwa tare tsakanin su da sauran ‘yan uwa daga sauran addinai.

Ya kuma yi addu’a ga Allah domin ci gaba da zaman lafiya, ci gaba, da kuma zaman lafiya na kasar.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya gargadi ‘yan Uwa Musulmai ga hidimar Azumin Watan Ramadan da aka fara.