Connect with us

Uncategorized

Ilimi Abin Fahariya! Bukata na Inje Karatu Kasar Waje, inji Yaron da Ya ci 347 a JAMB

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ekene Franklin, Dan Yaron da ya fiye kowa ga Jarabawan JAMB ta shekarar 2019, wada aka kamala makonnan da ta gabata ya bayyana da cewa baya son nasarar shi ta zama a banza.

Yaron ya fadi hakan ne bayan da ya gane da cewa shekarun sa sun kasa ga shiga makarantar da ya nemi shiga a Jarabawan JAMB din.

Naija News Hausa ta gane da cewa Ekene ya cika fom din JAMB ne da kuma kudurta neman shiga Makarantar Jami’ar UNILAG (University of Lagos), amma abin takaici, Dokar makarantar UNILAG bai bada dama ga dan shekara 15 da shiga makarantar ba, sai dai wanda ya kai ga shekara 16 zuwa sama bisa dokar su.

A yayin da Ekene ke jayayya da hakan, shugaban Hukumar Gudanar da Jarabawan Shiga Makarantar Jami’a Babba (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyode ya bada tabbacin dokar UNILAG da cewa lallai Ekene ba zai samu shiga makarantar ba bisa dokar su.

Ekene dan shekara 15 ne kawai ga haifuwa kuma ya nada muradin shiga UNILAG, amma doka ta hana hakan bisa tsawon shekarun sa. Sai dai Ekene bai raunana ga zuciyarsa ba.

Ya ce; “Ko da shike dokar UNILAG ya bayyana da cewa na kasa ga shekaru, ni kuma ban isa in canza masu doka ba. Duk da cewa ban san da dokar ba tun a farko, amma ina bada gaskiya cewa wani abu zai faru, wata kila wani ya taimaka mini a canza dokar” inji Ekene.

“Idan har UNILAG taki dauka na da shiga makarantar don karatu, ya zan dole a gareni in dakata har sai shekara ta gaba kamin in sake cika fom din, in kuma sake wata jarabawa.”

“Amma da zai fi kyau in samu wanda zai biya mini in fita zuwa kasar Turai don samun ilimin kimiyya wadatacce, ai da na karbi wannan da murna” inji Shi.

Ekene ya bayyana ga manema labarai da suka bukace shi da bayani cewa, Gurin sa ita ce ya samu taimakon daga wani wanda zai biya masa hidimar karatu a kasar Turai, inda zai samu wadataccen Ilimi a shafin Chemical Engineering a makarantar MIT.

Naija News Hausa na da sanin cewa Ekene ya saura a makarantar sakandiri, a wata Makarantar Sakandiri ta Jihar Imo, kuma bana ne zai rubuta jarabawan shi ta WAEC a watan Mayu/Yuli.

”Ba na son jarabawan JAMB da na rubuta ya zan a banza” inji Ekene.

Kalli Sakamakon Jarabawan JAMB ta shekarar 2019 da Ekene ya rubuta;

  • English           – 78
  • Mathematics  – 91
  • Physics           – 86 da kuma
  • Chemistry      –  92

Jimilar sakamakon jarabawan Ekene ita ce = 347