Uncategorized
An Kashe Wata ‘Yar Shekara Biyar Don Maganin Kudi a Zuru, Jihar Kebbi
0:00 / 0:00
Masu Maganin Kudi sun kashe wata ‘yar yarinya mai shekaru biyar a cikin kauyen Rikoto na karamar hukumar Zuru, a Jihar Kebbi.
Yarinyar, kamar yadda iyayenta da makwabta suka bayyana, an sace ta ne a yayin da ta ke kwance a saman tabarma a cikin filin gidan su da ke a Rikoto, saboda yanayin zafin da ake a ciki.
An bayyana da cewa a lokacin da kakarta wadda ke barci a gefenta ta kula da cewa yarinya ta ɓace, sai ta tada murya da janyo hankalin maƙwabta da shugabannin kauyan.
A cewar majiyar, “lokacin da suka ji mahaifiyar yarinyar da kakarta na kuwa da maimaita sunanta sai suka bar ta suka gudu, amma sun riga sun kashe ta kamin suka ajiye ta, suka kuma zubar da jinin yarinyar a cikin wata kwantena. Daga nan kuma suka gudu daga kauyan”.
An kuma bayyana cewa mutanen unguwar sun zagaya kauyan ko ta’ina, amma basu gana da su ba.
Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Kebbi (PPRO), DSP Nafiu Abubakar ya bada tabbacin kashe yarinyar.
Ya kara da cewa ‘yan sanda ba su kama kowa ba tukuna game da mumunar lamarin, amma da cewa hukumar su ta cigaba da bincike akan hakan.
Mu ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wani Saurayi ya Caka wa Malamar Asibiti Wuka a Jihar Kano, don ta hana shi Kwanci da ita.
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.