Uncategorized
Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood.
Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.
Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.
A bayan hakan ne aka gano wasu hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, inda jarumar ke cikin wani yanayi da shiga marar kyan gani na rashin da’a, tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.
Shugaban ya ce kungiyar na fuskantar matsala game da daukar mataki kan jarumar, Rahama Sadau. A yanayin da ya bayyana da mara kyan gani da kuma abin kyama wacce yake zargin jarumar ta yi akan ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.
Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.
“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta. Ba zamu saurara mata ba, Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano,” inji Yakasai.
“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin” Inji Shi.