Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Nasarawa sun kame ‘Yan Fashi 14

Published

on

Hukumar Jami’an tsaron ‘yan Sandan Jihar Nasarawa sun bayyana cewa sun kama mutane 14 da ake zaton su da zaman ‘yan fashin da ke tsoratar da sassan jihar.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Mista Bola Longe, ya bayyana hakan a lokacin da ake shigar da ‘yan fashin a hedkwatar hukumar, ranar Litinin da ta gabata a Lafia, babban birnin Tarayyar Jihar.

Longe ya bayyana cewa, an kama wadanda ake tuhumar ne a lokacin da suka kai wata hari a wajen buyar ‘yan fashin da ke a Mararaban-Udege, a karamar hukumar Toto, a karshen makon da ta gabata.

A cewar sa, wasu daga cikin mutanen da ‘yan fashin suka tara a baya sun iya gane wasu daga cikin ‘yan fashin da aka kame.
“Hukumar mu na a shirye don yaki da ta’addanci, fashi, hare-hare da sace-sacen mutane a Jihar Nasarawa.” inji Longe.
Ya kuma gargadi duk masu aiwatar da mugayen halayen da janye daga yin hakan ko kuma su kasance a shirye don shiga hannun jami’an tsaro.
“Muna bukatar hadin kan al’ummar jihar, musanman don sanar da duk wata alama da suka iya kula da shi da zai taimaka wa Jami’an tsaron don yaki da irin wadannan mugan halaye” inji Shi.