Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Operation Puff Adder suka kame ‘yan Hari da Makami 15 a Jihar Sokoto

Published

on

at

Yadda Hukumar Jami’an Tsaron Operation Puff Adder suka kame ‘yan Hari da Makami a Sokoto

Jami’an Tsaron rukunin ‘Yan Sandan Operation Puff Adder na Jihar Sokoto sun kame kimanin ‘yan hari da makami 15 a wurare daban daban a karamar hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

Kwamishinan’ yan sandan jihar Sokoto, Ibrahim Ka’oje, a yayin da ake gabatar da ‘yan hari da bindigar a hedkwatar ‘yan sandan Jihar Sokoto, ya bayyana cewa lallai an ci nasara da kame ‘yan harin ne da hadin gwiwar hukumomin tsaron Jihar duka a karshen makon da ta gabata.

A bayanin Ibrahim, “Mahara da bindigar sun gudo ne daga Jihar Zamfara sakamakon harin wuta da rundunar tsaron kasar ke kaiwa a kangin su da ke a Zamfara. Da suka gane da cewa ana cin nasara da su sai suka yi gudun hijira zuwa nan na Sokoto” inji shi.

Jami’an tsaro sun samu ribato miyagun makamai da bindigogi daga hannun ‘yan harin, hade ma da Babura, Mugan Maganin gargajiya da harsasun bindiga ire-ire.

Kwamishanan ya gargadi al’umar Jihar da sanar da duk wata motsi da alama da suka iya gane da ita da zai taimaka wa Jami’an tsaron wajen gana da ‘yan hari a kowace lokaci a Jihar.

Kalli wasu daga cikin hotunan ‘yan harin kamar yadda gidan talabijin yada labaran TVC suka rabar;